You are here: HomeAfricaBBC2023 08 11Article 1823258

BBC Hausa of Friday, 11 August 2023

Source: BBC

Liverpool za ta dauki Caicedo a matakin mafi tsada a Birtaniya

Moise Caicedo Moise Caicedo

Liverpool ta cimma yarjejeniyar sayen dan kwallon Brighton, Moise Caicedo kan fam miliyan 111 a matakin mafi tsada a Birtaniya.

Kodayake Chelsea ta yi ta kokarin sayen dan kwallon na Ecuador, bayan da Brighton ta ki sallama tayin da kungiyar Stamford Bridge ta yi tun farko.

Kuma tun farko an dauka dan wasan mai shekara 21 zai koma taka leda a Chelsea kan fara kakar bana.

Yanzu za a jira a gani ko Chelsea za ta biya sama da kudin da Liverpool ta amince za ta sayi dan kwallon kan fam miliyan 111.

Tun farko Brighton ta yi wa Caicedo farashin fam miliyan 100, yayin da ake cewar Chelsea ta taya dan wasan fam miliyan 80.

Kyaftin din Liverpool, Jordan Henderson da Fabinho sun koma buga gasar Saudi Arabia a watan jiya, amma kungiyar Anfield ta dauki Alexis Mac Allister daga Brighton a watan Yuni kan fam miliyan 35.

Henderson, mai shekara 33, ya koma Al-Ettifaq kan fam miliyan 12, yayin da Fabinho, mai shekara 29 ya koma Al-Ittihad kan fam miliyan 40.

Jerin 'yan wasan da aka saya mafi tsada a tamaula a duniya

1. Neymar Barcelona zuwa Paris St-Germain (2017) fam miliyan 200

2. Kylian Mbappe Monaco zuwa Paris St-Germain (2017) fam miliyan 165.7

3. Philippe Coutinho Liverpool zuwa Barcelona (2018) fam miliyan 142

4. Ousmane Dembele B. Dortmund zuwa Barcelona (2017) fam miliyan 135.5

5. Joao Felix Benfica zuwa Atletico Madrid (2019) fam miliyan 113

6. Enzo Fernandez Benfica zuwa Chelsea (2023) fam miliyan 107

7. Antoine Griezmann Atletico Madrid zuwa Barcelona (2019) fam miliyan 107

8. Declan Rice West Ham zuwa Arsenal (2023) fam miliyan 105

8. Jack Grealish Aston Villa zuwa Manchester City (2021) fam miliyan 100

10. Cristiano Ronaldo Real Madrid zuwa Juventus (2018) fam miliyan 99.2