You are here: HomeAfricaBBC2021 05 24Article 1268752

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Liverpool za ta buga Champions League a badi

Liverpool ta kammala kakar Premier League ta bana a mataki na uku a kan teburin Firimiya Liverpool ta kammala kakar Premier League ta bana a mataki na uku a kan teburin Firimiya

Liverpool ta kammala kakar Premier League ta bana a mataki na uku a kan teburin, bayan da ta doke Crystal Palace da ci 2-0 a Anfield ranar Lahadi.

Sadio Mane ne ya ci wa Liverpool kwallo biyun, wanda ya zura ta farko minti 34 da fara wasa, sannan ya ci na biyu saura minti 16 a tashi daga karawar.

Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 69 kenan a bana ta kuma karkare a mataki na uku, za ta wakilci Ingila a gasar Zakarun Turai ta Champions League ta badi.

Liverpool wadda ita ce mai kofin Premier a bara da ta lashe a karon farko tun bayan shekara 30 ta ci karo da kalubale a kakar bana, bayan da 'yan wasanta suka yi ta zuwa jinya.

Kungiyar ta Anfield ta karkare wasannin bana ba tare da lashe kowanne irin kofi ba, bayan da Real Madrid ta fitar da ita a Champions League na bana.

A kuma karawar ce Roy Hodgson ya ja ragamar Crystal Palace wasan karshe a kungiyar, bayan da ranar Talata ya sanar zai ajiye aiki a karshen kakar bana.

Hodgson ya fara horar da tamaula a Palace daga 12 ga watan Satumbar 2017, inda ya ja ragamar wasa 162 ya kuma ci karawa 54 da canjaras 38 aka doke shi wasa 70.

Chelsea ce ta yi ta hudu a teburin gasar Ingila, duk da rashin nasara da ci 2-1 da ta yi a Villa Park, hakan ya biyo bayan da Leicester ta sha kshi da ci 4-2 a King Power ranar Lahadi.