You are here: HomeAfricaBBC2023 09 01Article 1836314

BBC Hausa of Friday, 1 September 2023

Source: BBC

Liverpool ta yi watsi da tayin fam miliyan 150 kan Salah

Mohamed Salah Mohamed Salah

Liverpool ta ki amincewa da tayin fam miliyan 150 daga kungiyar Al-Ittihad ta Saudi Pro League kan dan wasan gaba Mohamed Salah .

An yi tayin dan wasan mai shekaru 31 a kan sama da fam miliyan 100, tare da karr-karen da za su kai fam miliyan 50.

Liverpool ta dage cewa dan wasan na Masar ba na siyarwa bane, kuma ba za ta motsa kan wannan matsayar ba.

Salah, wanda ya koma Reds daga kungiyar Roma ta Italiya a shekarar 2017, ya rattaba hannu kan sabuwar kwantiragi na shekaru uku a bazarar da ta gabata.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce a makon da ya gabata Salah ya jajirce 'dari bisa dari' a kungiyar ta Anfield, kuma a ranar Juma'a ya sake jaddada matsayin kulob din na cewa dan wasan ba ya kasuwa.