You are here: HomeAfricaBBC2023 09 17Article 1845893

BBC Hausa of Sunday, 17 September 2023

Source: BBC

Liverpool ta hada maki uku a gidan Wolverhampton

Hoto daga gasar Hoto daga gasar

Liverpool ta yi wasa biyar a Premier League ba tare da rashin nasara ba a kakar bana ta 2023/24.

Kungiyar ta Anfield ta je ta doke Wolverhampton 3-1 a Molineux a fafatawar ta babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wolves ce ta fara cin kwallo minti na bakwai da take leda a karawar da Andy Robertson na Liverpool ya buga wasa na 200 a Premier League.

Minti 10 da suka koma zagaye na biyu bayan hutu ne Liverpool ta farke ta hannun Cody Gakpo, sannan Robertson ya ci na biyu da kuma ta uku da Hugo Bueno da ya ci gida.

Salah wanda ya bayar da kwallo biyu aka zura a raga, ya zama ɗan wasa na hudu da ya bayar da kwallo aka zura a raga a waje a karawa biyar a jere.

Masu rike da wannan bajintar sun hada da Muzz Izzet da Cesc Fabraegas da kuma Gerard Deulofeu.

Kenan Liverpool ta yi wasa 16 ba tare da an doke ta ba tun bayan rashin nasara 4-1 a hannun Manchester City ranar 1 ga watan Satumba.

Kafin wannan fafatawar, Liverpool ba ta iya cin sa cin wasannin da take bugawa a ranar Asabar da rana, cikin wasanni shida da ta buga a baya ta yi canjaras uku an kuma doke a karawa uku.