You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848632

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

Liverpool ta doke LASK a Europa League

Yan wasan Liverpool Yan wasan Liverpool

Liverpool ta fara gasar Europa League na bana da kafar dama inda ta lashe wasanta na farko a matakin rukuni bayan da ta doke LASK ta ƙasar Austria da Ci 3-1.

Ɗan wasan tsakiya na LASK Florian Flecker ne ya fara jefa kwallo a ragar Liverpool a minti na 19 da fara wasa.

Darwin Nunez ya rama kwallon da aka ci Liverpool a bugun fenariti bayan da aka yi wa Luis Diaz keta, kafin Diaz da kansa ya zura kwallo ta biyu da taimakon sabon ɗan wasan Liverpool Ryan Gravenberch.

Mohammed Salah wanda ya shigo wasan bayan hutun rabin lokaci ya jefa wa Liverpool kwallonta na uku domin tabbatar da nasara a wasan.

Klopp ya yi canje-canje 11 a kungiyar da ta fara karawa da Wolves a wasansu na baya.