You are here: HomeAfricaBBC2023 03 10Article 1728650

BBC Hausa of Friday, 10 March 2023

Source: BBC

Lionel Messi ya fi son zama a PSG - Guillem Balague

Lionel Messi Lionel Messi

Lionel Messi zai ci gaba da kasancewa dan kwallon Paris St-Germain a kakar wasa mai zuwa amma dole sai an tabbatar masa cewa kungiyar za ta yi gogayya da wadansu manyan a Turai, in ji dan jarida Guillem Balague.

Dan Argentina mai shekaru 35, yarjejeniyarsa za ta kare ne a karshen kakar wasan bana a Faransa, amma akwai damar ya sabunta ta har zuwa 2024.

Gawurtaccen dan kwallon ya ci kwallo 29 a wasa 64 da ya buga wa PSG tun bayan da ya bar Barcelona, shekaru biyu da suka wuce.

An fitar da PSG daga gasar zakarun Turai bayan ta sha kashi a hannun Bayern Munich a wasan zagaye na biyu.

Messi ya zura kwallo 672 a wasa 778 da ya buga wa Barcelona - kungiyar da ya soma murza wa leda tun yana da shekaru 13, sannan kuma ya lashe kofuna 35.