You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716410

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Lewandowski ne kan gaba a cin kwallaye a La Liga

Robert Lewandowski Robert Lewandowski

Robert Lewandowski na Barcelona shine kan gaba a yawan cin kwallaye a La Liga, bayan da aka buga karawar mako na 21.

Lewandowski wanda ya koma Barcelona kan fara kakar nan ya zura 14 a raga a La Liga a karawa 17 da ya yi.

Ya fara cin kwallo biyu ranar 21 ga watan Agustan 2022 a gasar a fafatawa da Real Sociedad.

Sau hudu Lewandowski ya zura kwallaye bibiyu a La Liga ta kakar nan, wanda ya karbi jan kati a wasa daya a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Ranar 8 ga watan Nuwamba a wasan Barcelona da Osasuna aka yi wa Lewandowski jan kati.

Barcelona wadda take ta daya a teburin La Liga za ta karbi bakuncin Cadiz ranar Lahadi, yayin da Real za ta fafata da Osasuna ranar Asabar.

Idan Real ta ci Osasuna za ta rage tazarar maki takwas tsakaninta da Barcelona zai koma biyar, kafin kungiyar Nou Camp ta yi wasa ranar Lahadi.

Jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga

  • Robert Lewandowski FC Barcelona 14


  • Joselu RCD Espanyol 11


  • Karim Benzema Real Madrid CF 11


  • Borja Iglesias Real Betis 9


  • Alexander Sorloth Real Sociedad 9


  • Iago Aspas Celta de Vigo 9


  • Vedat Muriqi Real Mallorca 8


  • Oihan Sancet Athletic de Bilbao 8


  • Ezequiel Avila Osasuna 7


  • Vinicius Junior Real Madrid CF 7


  • Alvaro Morata Atletico de Madrid 7


  • Enes Unal Getafe CF 7


  • Brais Mendez Real Sociedad 7


  • Wasannin mako na 22 da za a fara a La Liga:

    Juma'a 18 ga watan Janairu

  • Girona da Almeria Match details


  • Asabar 18 ga watan Janairu

  • Real Sociedad da Celta de Vigo


  • Real Betis da Real Valladolid


  • Real Mallorca da Villarreal


  • Osasuna da Real Madrid


  • Lahadi 19 ga watan Janairu

  • Elche da RCD Espanyol


  • Rayo Vallecano da Sevilla


  • Atletico Madrid da Athletic Bilbao


  • FC Barcelona da Cadiz


  • Getafe da Valencia