You are here: HomeAfricaBBC2021 06 07Article 1280500

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

Lafiya Zinariya: Amfanin shayarwa ga mai jego kashi na biyu

Lafiya Zinariya wata shiri ne na BBC mei kula da lafiyan mata Lafiya Zinariya wata shiri ne na BBC mei kula da lafiyan mata

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:



Shayarwa na taimaka wa uwa wajen komawar mahaifa tare da kare ta daga kamuwa da cutar daji ko kansa.

Haka kuma yana kare masu jego daga fadawa matsananciyar damuwa.

Mujallar kiwon lafiya ta Pediatrics, wadda kungiyar likitocin yara ta Amurka AAP, ta yi bayyani kan amfanin da uwa za ta samu idan tana shayar da jaririnta.

Wata makalar da aka sabunta a shekarar 2012 wadda aka wallafa a shafin intanet.

Inda ta bayyana cewa shayar da nonon uwa ita ce hanya mafi dacewa ta ciyar da jariri.

Kuma ta wannan hanyar ce jariri zai samu kayayyakin gina jikin da ya ke bukata.

  • Amfanin shayarwa ga mai jego
Wasu daga cikin amfanin da mai shayarwa za ta samu a cewar makalar, sun hada da jinin bikinta zai ragu.

Haka kuma matan da basu taba samun ciwon suga a lokacin da suke da juna biyu ba, za su samu raguwar hadarin kamuwa da ciwon nau'i na biyu.

Bincike ya nuna cewa shayarwa na tsawon kowace shekara daya yana rage hatsarin kamuwa da ciwon suga nau'i na biyu da kashi hudu cikin dari zuwa kashi 12 cikin dari.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa wani bincike da aka yi ya nuna cewa matan da suka shayar na tsawon wata 12 zuwa wata 23 sun samu raguwar cutar hawan jini sosai.

Haka zalika kungiyar ta kara da cewa ana samun karuwar matsananciyar damuwa a tsakanin masu jegon da basa shayarwa ko matan da suke yin yaye da wuri.

Inda ta jaddada muhimmancin shayar da nonon uwa musamman bayar da shi zalla na tsawon wata shida.