You are here: HomeAfricaBBC2023 01 30Article 1704788

BBC Hausa of Monday, 30 January 2023

Source: BBC

La Liga: Real Madrid ta sake haduwa da cikas

Kocin Real Madrid Carlo Ancelloti Kocin Real Madrid Carlo Ancelloti

Real Madrid ta kara haduwa da cikas a kokarinta na kamo abokan hamayyarsu wato Barcelona, bayan da suka tashi ba bu ci da Real Sociedad har gida.

Hakan na nufin a yanzu tazarar da Barcelona da ke kan teburin na La Liga ta basu, ta tashi daga maki uku zuwa biyar.

Kungiyar ta Nou Camp ta ci wasanta ne a Girona, da hakan ya bata damar hada maki uku.

A yanzu Madrid na ci gaba da zama na biyu, maki uku tsakaninta da Real Sociedad.

A wasan da aka yi a Bernabeau, Madrid ta zubar da damarmaki musamman ta hannun dan wasanta na gefe, Vinicius Junior.

To amma golan Real Sociedad Alex Remiro ne ya nuna kansa, inda ya cire kwallaye masu hadari da aka buga masa.

A wata mai kama da haka, abokan hamayyar Madrid da suke makwabtaka wato Atletico Madrid, na zaune ne na hudu a teburin na La Liga, bayan da suka tashi 1-0 da Osasuna ta hannun Saul Niguez.

A sauran wasanni, Valencia ta sha kashi hannun Valladolid 1-0, sai kuma Celta Vigo da ta ci Athletic Bilbao itama 1-0.