You are here: HomeAfricaBBC2023 07 04Article 1797860

BBC Hausa of Tuesday, 4 July 2023

Source: BBC

Kyogo Furuhashi ya ƙara tsawaita kwantaraginsa a Celtic

Kyogo Furuhashi Kyogo Furuhashi

Ɗan wasan gaban Japan Kyogo Furuhashi ya ƙara tsawaita kwantaraginsa a Celtic da shekara huɗu, yana cewa ya "ji daɗi" kuma zai taimaka wajen kare kofuna uku da ƙungiyarsa ta lashe.

Mai shekara 28 ɗin ya ci kwallo 54 a wasa 83 tun bayan zuwansa Celtic Park daga Vissel Kobe a 2021.

Ƙoƙarin da Kyogo ya riƙa yi yasa aka yi ta yaɗa jita-jitar zai bi tsohon kocinsa Ange Postecoglou zuwa Tottenham.

Amma ya shaida wa shafin Celtic na intanet cewa zai ci gaba da aiki da sabon kocin da aka kawo Brendan Rodgers.

"Babban koci ne, ya san ƙungiyar ya san me ake yi a samu nasarar lashe kofi," in ji Kyogo.

Labarin tsawaita kwantaragin ya zo ne bayan da Celtic ta sayar da ɗaya daga cikin manyan 'yan wasanta masu ƙoƙari, ɗan wasan Portugal Jota zuwa ƙungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya kan kuɗin da ba a bayyana ba.

Kyogo da kwantaraginsa ta farko za ta ƙare a 2025, an zaɓe shi ɗan wasan gasar Scotland na shekarar da ta gabata, wani abu da ya ce bai taɓa zato ba.