You are here: HomeAfricaBBC2023 04 19Article 1751684

BBC Hausa of Wednesday, 19 April 2023

Source: BBC

Kungiyoyin da aka ci kwallaye amma suka kai zagayen gaba a Champions

Hoton alama Hoton alama

Yana da wahala a zura wa kungiya kwallo uku ko fiye da haka a wasan farko a kowacce irin gasa ta gida da waje, amma ka farke ta kai zagayen gaba a fafatawa ta biyu.

A gasar Zakarun Turai an samu kungiyoyin da aka ci kwallo da yawa a zagayen farko, amma suka sa kwazo a karawa ta biyu suka kai zagayen gaba.

Kungiyoyi hudu ne suka kai zagayen gaba a Champions League, duk da an zura musu kwallo uku a kalla ko fiye da hakan a wasan farko.

Manchester City ta doke Bayern Munich 3-0 a wasan farko zangon quarter finals ranar 13 ga watan Afirilu a Eihad.

Ko kungiyar Jamus za ta zama ta biyar da aka ci kwallo uku, sannan ta farke ta kai zagayen gaba a Champions League?

Ga rahoton da Mohammed Abdu ya hada.

Wasannin da aka ci kwallaye da yawa a karawar farko aka soke su a wasa na biyu:

Wasan farko shine tsakanin Deportivo La Coruna da AC Milan a quarter finals

Sun buga wasan a kakar 2003/04, inda Deportivo ta kai zagayen gaba.

Fafatawar farko Talata 23 Maris 2004

AC Milan 4 : 1 Deportivo La Coruna

Minti 11 da fara wasa kungiyar Sifaniya ta fara zura kwallo a raga ta hannun Walter Pandiani.

Daga baya Milan ta ci hudu ta hannun Ricardo Kaka da Andriy Shevchenko, sannan kaka ya kara na biyu, Andrea Pirlo ya zura na hudu.

Fafatawa ta biyu Laraba 7 ga watan Afirilu 2004

Deportivo La Coruna 4 : 0 AC Milan

Wadanda suka ci wa kungiyar Sifaniya kwallayen sun hada da Walter Pandiani da Juan Carlos Valeron da Albert Martos Luque da kuma Francisco Figueroa Alonso Fran

Wasa na biyu Barcelona da Paris Saint-Germain zagayen 'yan 16

Sun buga wasan a kakar 2016/17, inda Barcelona ta kai zagayen gaba

Fafatawar farko Talata 14 ga watan Fabrairun 2017

  • Paris Saint-Germain 4 : 0 Barcelona


  • PSG ta ci kwallo ta hannun Angel Di Maria da Julian Draxler, sai Angel Di Maria ya kara na uku, sannan Edinson Cavani ya zura na hudu a raga.

    Fafafatawa ta biyu Laraba 8 ga watan Maris 2017

  • Barcelona 6 : 1 Paris Saint-Germain


  • Minti uku da take leda Luis Suarez ya ci Barcelona kwallon farko, sai Layvin Kurzawa ya ci gida, Lionel Messi ya ci da fenariti, neymar ya zura biyu a raga har da a bugun fenariti, sannan Sergi Roberto ya kara na shida

    PSG ta ci kwallo ta hannun Edinson Cavani a minti na 62.

    Wasa na uku Roma da Barcelona a zagayen quarter finals

    Sun fafata a kakar 2017/18, yayin da Roma ta kai zagayen gaba

    Fafafatawar farko Larabar 4 ga watan Afirilun 2018.

  • Barcelona 4 : 1 Roma


  • Daniele De Rossi ya fara cin gida a minti na 38 da fara wasa, sai Kostas Manolas shima ya ci gida daga nan Gerard Pique ya kara na uku, sannan Luis Suarez ya ci na hudu.

    Roma ta ci kwallo ta hannun Edin Dzeko

    Fafatawa ta biyu Talata 10 ga watan Afirilun 2018

  • Roma 3 : 0 Barcelona


  • Minti shida da fara wasa Edin Dzeko ya fara cin kwallo, sai Daniele De Rossi ya kara na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sannan Kostas Manolas ya ci na uku.

    Wasa na hudu Liverpool da Barcelona a karawar daf da karhe

    Sun kece raini a kakar 2018/19, yayin da Liverpool ta kai zagayen gaba

    Fafatawar farko Laraba 1 ga watan Mayu 2019

  • Barcelona 3 : 0 Liverpool


  • Luis Suarez ne ya fara zura kwallo a raga, sannan Lionel Messi ya ci biyu a wasan.

    Fafatawa ta biyu Tuesday 7 May 2019

    Liverpool 4 : 0 Barcelona

    Minti bakwai da take leda Divock Origi ya fara cin kwallo, sai Georginio Wijnaldum ya kara na biyu a minti na 54, minti biyu tsakani ya kara na uku, sannan Divock Origi ya kara na hudu, saura minti 11 a tashi daga wasan.

    Bayern Munich na fatan ta zama ta biyar da za ta yi wannan bajintar.

    A karawa 24 a gasar da ake fara cin Bayern a fafatawar farko ta kai zagayen gaba sau 10.

    Na karshe da ta yi hakan shine a wasa da Porto a Champions League a kakar 2014, inda kungiyar Portugal ta ci 3-1 a Jamus, Bayern ta ci 6-1.

    The last time this happened was against Porto in the 2014/15 UCL campaign, when they bounced back from a 3-1 reverse in the first leg with a 6-1 triumph at home.