You are here: HomeAfricaBBC2023 08 12Article 1823303

BBC Hausa of Saturday, 12 August 2023

Source: BBC

Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Tata

Sheikh Ibrahim Tata Sheikh Ibrahim Tata

Cikin shirin Ku San Malamanku na wannan mako BBC ta tattauna da Sheikh Ibrahim Tata.

An haifi Sheikh Ibrahim Tata a unguwar Tudun Wada da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya a shekarar 1970.

Karatunsa

Shehin Malamin ya ce ya fara karatun addini a wajen mahaifinsa tun yana ɗan ƙarami.

''A wajensa na yi babbaƙu, na yi farfaru, domin kuwa a tsarinmu a lokacin duk wanda ya taso sai ya yi karatu na addini'', in ji malamin.

Malamin ya shiga makarantar furammare ta Muhammad Kabir, a shekarar 1979 zuwa 1985.

Sannan ya zarce makarantar sakandire da Sardauna Memorial Collage a garin Kaduna zuwa 1991.

Ya kuma halarci shahararriya makarantar fasaha ta Kaduna wato Kaduna State Polytechnic a shekarar 1995, inda ya karanmta fannin mulki.

Malamin ya sake komawa makarantar a shekarar 1998 domin karatun babbar diploma, inda ya kammala a shekarar 2000.

Malamansa

Malamain ya ce malamainsa na farko da ya fara koyon karatun addinmi a wajensa shi ne mahaifinsa, sannan ya yi karatun wasu littafan addini a wajen wani aminin mahaifinsa Malam Musa, sannan ya yi karatu a wajen Malam Hassan Maidori, da sheikh Bashir Nuhu Assalafiy

Limanci

An zabi Sheihk Ibrahim tata amatsayin babban limamin masallacin babbar kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da ke Kaduna

Abin farin ciki

Malamin ya ce ranar farin cikin da ba zai taba mantawa da ita ba a rayuwarsa ita ce ranara da ka ba shi limancin masallacin Juma'a.

Sannan kuma ya ce babban abin da ke faranta masa rai shi ne karatun Al-qur'ani da hadisai da sauran karatuttukan malamai.

'Tambayar da ake yawan yi min'

Sheikh Ibrahim Tata ya ce tambayoyin da aka fi yi masa su ne tambayoiyin da suka shafi fiqihu

'Abin da ke ɓata min rai'

Malamin ya ce babban abin da ke ɓata masa rai shi ne ya ji Malami ya sanya baki a cikin harkar da ba ta shafe su ba .

''Ko ya bayar da fatawa kan abin da ba shi da ilimi a kai'', in ji malamin

Wasannin ƙuruciya

Malamin ya ce a lokacin yake yarinta babu wasan da ya fi so irin ƙwallon ƙafa, ya kuma ce shi ɗan wasan ƙwallon kafa ne a lokacin da yake yaro, yana mai cewa abokansa na ƙuruciya za su iya shaida haka.

'Surar da na fi jin daɗin karantawa'

Sheikh Ibrahim Tata ya ce surar da ya fi jin daɗin karanta ta a cikin al-qur'ani ita ce suratul- Muhammad, saboda abin da ta ƙunsa na abin da ya shafi bayani kan Manzon Allah (S.A.W) da sahabbansa, ''musamman ayar da ke ƙarshen surar''.

'Hadisin da ya fi faranta min rai'

Hadisin da ya fi faranta ran malamin shi ne hadisin Umar bin Khaddan R.A na ''Inna mal'amalu bin niyati'' wanda shahararren hadisi ne.

'Babban burina'

Babban burin malamin shi ne karantar da al'umma domin kawar musu da shubuha, kamar yadda ya bayyana.