You are here: HomeAfricaBBC2021 03 26Article 1215706

BBC Hausa of Friday, 26 March 2021

Source: bbc.com

Ku San Malamanku tare da Sheikh Dokta Ibrahim Disina

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Bauchi Sheikh Dokta Ibrahim Disina ya ce sabanin fahimta da na aƙida ba sa hana shi mu'amala da kowane irin musulmi.

Dokta Disina ya ce tun da Allah bai hana shi mu'amala da wanda suke da saɓani a addini ba, to babu dalili da zai sa ya ƙi yin mu'amala da mabiyin dariƙun sufaye ko kuma wani da suke da saɓanin fahimta.

Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da BBC a cikin shirin Ku San Malamanku. Ya ce yana alaƙa da duk wanda alaƙa ta kama a yi da shi a cikin dukkan bangarori.

Sheikh Disina ya ce a cikin waɗanda yake hulɗa da su har da ƴan shi'a waɗanda suka taso tun suna yara, kuma har yanzu suna ci gaba da mu'amala.

Sai dai ya ce alaƙar ba ta sa ya ɓoye aƙidarsa ko fahitarsa a kan wani abu da addini.

Wane ne Sheikh Ibrahim Disina?

Sheikh Ibrahim Adam Disina na daga manyan malaman addinin Musulunci da ke jihar Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya.

An haifi malamin a shekarar 1978 a garin Disina na karamar hukumar Shira a jihar ta Bauchi. Ya fara karatun allo da na piramare a garin Disina. Daga nan kuma ya tafi garin Bauchi domin ci gaba da karatun sakandare. Kuma daga nan ne ya fara katarun addinin ka'in da na'in.

Bayan kammala karatun sakandare ya tafi kwalejin ilimi ta garin Misau inda ya yi diploma. Sannan ya samu damar tafiya zuwa Jami'ar Musulunci ta Madina inda ya yi digiri na farko a fannin hadisi.

Ya yi digiri na biyu a jami'ar Jos, sannan ya yi digiri na uku a Jami'ar Usman Dan Fadiyo da ke Sokoto.

Dokta Ibrahim Disina ya ce ya tasirantu da malamai da dama ciki da wajen Najeriya, wadanda suka ba shi gudunmuwa a harkar neman ilimi.

Cikin malaman akwai Limamin garin Dushin Malam Yuguda a garin Disina, da Malam Ahmad Usman da Malam Salisu Zakariyya da Malam Ahmad Tijjani.

A ƙasar Saudi Arabia ma, Sheikh Disina ya ce ya fa'idantu da malamai da dama, musamman a jami'ar Musulunci ta Madina.

Gwanayensa a malaman Najeriya

Sheikh Ibrahim Disina ya ce akwai wasu malamai a Najeriya da yake dauka a matsayin taurari, kuma suka zame masa gwaraza.

Daga cikinsu akwai Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, wanda ya ce ya yi matukar tasiri a rayuwarsa ta ilimi.

Malam Disina ya ce ya ja wa Sheikh Jaafar baki har ya sauke wasu litattafai guda bakwai a garin Bauchi.

Haka kuma Malam Disina ya ce yana fata ya samu dimbin ilimi da bincike irin na Dokta Muhammad Sani Rijiyar Lemo.

A bangaren wayewa da dattako da faran-faran da jama'a kuwa, ya ce yana fata zama kamar Dokta Bashir Aliyu Umar.

A fannin iya mu'amala da jama'a da hukumomi kuwa yana fata ya zama kamar Dokta Abubakar Sani Birnin Kudu.

Idan kuwa a jajircewa ne da gwagwarmaya da baiwar rubutu, Dokta Disina ya ce yana fata ya zama kamar Farfesa Mansur Sokoto.

Sana'o'insa a ƙuruciya

Sheikh Ibrahim Disina ya ce ya yi sana'o'i da dama a kuruciyarsa, wasu saboda kiriniya irin ta yara, wasu kuma domin ya samu damar daukar nauyin karatunsa.

Daga cikin sana'o'in da malamin ya ce ya yi akwai dako da aikin lambu, da kamun kifi.

Ya ce daya daga abin da ba zai manta da shi ba a kuruciya akwai yaron mota, wato kwandasta. Ya yi wannan sana'ar ne a Kano inda yake bin mota tsakanin Sheka - Rimi - Asibiti.

Amma a yanzu, Dokta Ibrahim Disina babban manomi ne a jihar Bauchi, inda yake hada noma da kiwon dabbobi har ma da kiwon kifi.

Wasu batutuwa a taƙaice

Babban abin farin ciki da ya faru da Dokta Disina wanda ya ce ba zai taba mantawa ba, shi ne lokacin da Sheikh Jaafar Mahmud Adam ya aika a fada masa cewa ya samu gurbin karatu a Jami'ar Musulunci ta Madina.

Babban abin bakin cikin da ba zai manta da shi ba kuma shi ne lokacin da ya samu labarin cewa an yi wa Sheikh Jaafar kisan gilla

Surar da ta fi ba shi wahala ita ce Suratul An'am

Surar da ya fi so kuma ita ce Suratussaffat

Tambayoyin da aka fi yi masa su ne kan aure da sakin aure

Abincin da ya fi so shi ne Dan Wake

Matansa hudu da ƴaƴa fiye da goma

Manyan burikansa a duniya guda biyu ne. Na daya tsayawar tashar Sunnah TV da kafafunta. Na biyu kuma kammala ginin makarantar da ya fara ginawa sannan ya sa mata sunan daya daga malamansa a Madina Sheikh Zarban.

Join our Newsletter