You are here: HomeAfricaBBC2021 05 25Article 1269910

BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Ku San Malamanku tare da Malam Abubakar Saminaka Yauri

Malam Abubakar Saminaka Yauri Malam Abubakar Saminaka Yauri



Abubakar Muhammad Saminaka Yauri malamin Musulunci ne da ya ƙware a harshen Larabci da Fiƙihu da kuma Usulul Fiƙihi, kamar yadda ya shaida wa BBC a cikin shirin Ku San Malamanku na wannan makon.

Shehin malamin wanda ya fi shahara da Malam Saminaka, an haife shi ranar 22 ga watan Oktoban 1972 a garin Saminaka na Ƙaramar Hukumar Yauri ta jihar Kebbi a Najeriya.

Malam ya yi karatu a gaban malamai da dama da suka haɗa da Malam Usman a garin Zaria, inda ya karanta litattafan Fiƙihu kamar Ahalari zuwa Muktasar da kuma waƙoƙin yabo irinsu Ishiriniya da Alburdah.

Neman ilimiMalam Saminaka ya yi karatun firamare a mahaifarsa, sai dai bai samu shiga sakandare da wuri ba saboda mahaifiyarsa ta yi fargabar cewa bai yi girman da zai iya barin gida ba domin shiga makarantar kwana.

"Daga nan ne kuma aka samu tsaiko, saboda yayyena biyu suna bayar da labarin yadda manyan ɗalibai ke aikata musu a makarantar kwana idan sun zo gida, shi ne hajiya (mahaifiya) ta ce ba zan je ba har sai na ƙara ƙwari," in ji shi.

Bayan ya koma gida daga Zaria ne kuma sai mahaifinsa ya shaida masa cewa dole ya yi karatu domin ya yi aiki ko kuma ya nemi sana'a, abin da ya sa ya koma garin Argungu kenan a 1992, inda ya kammala sakandare.

Bayan kammala sakandare, Malam ya shiga Kwalejin Ilimi ta Adamu Audi Argungu kuma ya samu shaidar karatu ta NCE.

Malam Saminaka ya ce ya yi bara sosai a Zaria kuma ya sha wahala sosai kamar ko wane almajiri amma ya ce wannan bai kai ilimin da ya samu ba.

Ya nemi gurbi a Jami'ar Usma Danfodiyo da ke Sokoto har sau uku amma ba tare da ya yi nasara ba.

Daga baya malamin ya je Jami'ar Afirka da ke birnin Khartoum a Sudan, inda ya yi digiri a ɓangaren shari'a, sannan ya je kwalejin Peace College ya samu digiri kan fassara. Ya yi digiri kan harshen Larabci a Jami'atu Duwalil Arabiyya duk a Sudan.

Kazalika, Malam Saminaka ya yi digiri na biyu a Jami'ar Sinar kuma yanzu haka yana ƙoƙarin kammala digiri na uku duka a harshen Larabcin.

Haka nan, ya yi digiri na biyu a fannin alaƙar ƙasashe, wanda yake matakin kammalawa yanzu haka.

Malam ya yi difiloma a fannin Hadisi a Jami'ar Jazira, sannan ya yi karatu kan hulɗa da jama'a da aikin jarida a Jamia'r Ma'amun Umaida.

Malam na koyarwa a birnin na Khartoum a halin yanzu.

Malamansa

Malam Saminaka ya ce akwai malamai da dama da suka yi tasiri sosai a rayuwarsa amma ya ce ba kamar Malam Usman wanda ya ce ya zauna a wurinsa a Zaria kuma ya rike shi bisa amana.

"Malam ya yi tasiri sosai a rayuwata wanda ya sa a lokacin da na bar Zaria, bayan na shaida wa mahaifina cewa na gaji da zaman garin. To da na koma gida na kan ji sautin muryar Malam Usman yana rera karatu saboda kewarsa da nake yi," a cewarsa.

Ɓangaren da ya fi ƙwarewa a karatu

"Wani lokaci sai in ga kamar na fi fahimtar Fiƙihu sosai, amma ina ganin na fi kwarewa a ɓangaren Lugga ko usulul Fiƙihi," a cewar Malam.

Amma ya ce ya fahimci Nahawu sosai da Hadisai ma. Don yana karatu ma a bangaren Hidisi kuma yana karantar da shi.

Iyalii

Malam Abubakar Muhammad Saminaka na da mata biyu - Hafsatu Abdullahi mai 'ya'ya 13 da kuma Hauwa'u Abubakar mai 'ya'ya huɗu.

Malam ya ce yana da jikoki.