You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848656

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

'Kowane dare sai na yi mugayen mafarkai kan girgizar-ƙasa'

Malak da Jamila Malak da Jamila

Sama da wata guda ke nan bayan afkuwar mummunar girgizar-ƙasa a Moroko, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 3,000.

A bayyane yake cewa za a ɗauki tsawon lokaci kafin a warke daga bala'in da mutane da dama suka shiga sakamakon girgizan ƙasar.

A cikin wannan yanayin, muryoyin waɗanda girgizar-ƙasar ta shafa kamar Malak, ƴar shekara 12 ta bayyana mummunan halin da suke ciki kasancewa ita da wasu yara da dama na zama ne cikin tanti na wucin gadi.

"Na matsu na bar wannan wurin, muna shan wahala" in ji Malak.

Malak ta kasance ita ce babba cikin ƴan'uwanta huɗu kuma babu ɗaya daga cikin su da ke zuwa makaranta bayan da girgizar ƙasar ta ɗaiɗaita garinsu, Amizmiz da ke tsakiyar tsaunukan Atlas.

Ƙauyukan da suka fi nisa daga gari ne suka fi fuskantar bala'in girgizar-ƙasar.

Masu kai taimako sun kasance suna fuskantar ƙaluabale wajen kai agajin gaggawa ga waɗannan ƙauyukan saboda hanyoyi da dama sun toshe sakamakon zaftarewar kasa da ta biyo bayan girgizar ƙasar.

'Ina kewar makaranta'

Yayin da muka zagaya garin Amizmiz, mai tazarar kilomita 50 kudu maso yammacin Marrakesh, mun ga tantunan da yawa waɗanda iyalan da lamarin ya tagayyara suke zama a ciki, wanda hakan ya sa suka shiga cikin mummunar damuwa kan yadda abin zai kasance lokacin sanyi.

"Muna buƙatar abinci da kuɗi da kuma abu mafi muhimmanci, gida" in ji Malak.

Ta ce tana jin takaici idan ta tuna da cewa ba ta zuwa makarata sakamakon girgizar ƙasar. "Makomata tana cikin haɗari," in ji ta yayin da take bayyana burinta na zama likitar hakori.

Ta yaba da ƙwazon mahaifiyarta wajen renon ta da ƴan'uwanta: "fatana shi ne na girma, na samu aikin yi kuma ni ma na cika mata burinta" in ji ta, cikin baƙin ciki.

Mummunan mafarki

Na ɗauki tsawon lokaci cikin tantunan da gwamnatin Moroko ta samar na wucin-gadi ina tattaunawa da iyalan Malak.

Kuma ga dukkan alama ƙanwar Malak, Doaa har yanzu tana cikin tsoro da firgici.

"Kullum da dare sai na yi mafarkin girgizar ƙasar, abin na da ban tsoro" in ji Doaa, ƙanwar Malak.

"Wani lokacin idan na farka daga barci, sai na ji ƙasa tana girgiɗi."

Mutane da dama da na tattauna da su, labarin abin da suka fuskanta iri daya ne da na Malak da ƙanwarta Doaa.

Asusun talafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya (Unicef) ya ce kusan yara 100,000 ne mummunar girgizar kasar ta Moroko ta shafa.

Ta yi gargadin cewa za a ci gaba da fuskantar rushe-rushe sakamakon girgizar ƙasar a cikin kwanaki da makonni masu zuwa, wanda zai jefa yara da iyalai cikin tsananin damuwa.

A wani sansanin, Jamila, ɗaya daga cikin yaran da ke rayuwa yanzu a cikin tanti ta ce:

"Muna cikin wahala sosai, yawancin kayan agajin da suka isa sansanin, ‘yan sa kai sun rabe su."

Jamila ta ƙara da cewa: "Ba mu da ban-ɗaki a nan."

"Ina tsoron kada mu fara rashin lafiya a nan, dukkan mu a gajiye muke."

Yawancin iyalai da ke sansanin matalauta ne kuma tuni suka fara fafutukar samun abin dogaro da kai, girgizar kasar dai ta ƙara jefa waɗannan mutane cikin wahala.

'Girgizar ƙasar tamkar tashin ƙiyama'

Ikhlas, ƴar shekar 10 ta ba ni labarin daren da girgizar ƙasar ta afku.

"Ina zaune kawai na ji kamar kasa na girgiɗi, kawai sai na ruga wajen babana kuma na yi ta karatun ayoyi daga cikin Al-ƙur'ani.

"Na ji tamkar tashin ƙiyama ne ya zo."

Tun daga lokacin ta kasance cikin tsoro.

Ta nuna min makarantarta, amma babu abin da ya rage sai ɓaraguzan ginin makarantar kawai.

Kamar Malak, ita ma Ikhlas tana kewar makarantar.

"Ina son na ga malamata da abokanaina" in ji Ikhlas.

'Muna buƙatar kayan kwalliya ba kayan abinci kaɗai ba'

Yayin da muke shirin barin sansanin, wata mata ta tambaye ni a hankali: "Shin ko kina da jan-baki, ko turare? Ina so na yi kyau kuma na dinga ƙamshi"

Kalamanta abin ban tausayi, buƙatar na iya zama da ban mamaki, amma ba kasafai ake saka kayan bayan-gida da kayan kwalliya a cikin duk wani kunshin agaji da ake bai wa iyalan waɗanda abin ya shafa a Moroko ba.

Mata na iya jin kunyar tambayar irin waɗannan kayyayakin, Amma mutane na buƙatar fiye da abinci ko barguna.

Sau da yawa ana yin watsi da wannan batu idan ana batun bayar da agaji ga wadanda bala'o'i daban-daban suka shafa musamman a kasashen Larabawa.

Hukumomin kasar Moroko sun ce suna yin iyakar bakin ƙoƙarinsu domin ganin an rage wa waɗanda lamarin ya shafa raɗaɗi, amma ana ɗaukar lokaci, saboda girgizar kasar ba ƙaramar ɓarna ta yi ba.

Tuni aka kafa ajujuwa na wucin-gadi a wasu wuraren da abin ya shafa.

Sarkin ƙasar ya sanar da wani shirin sake gina gidaje 50,000 da suka lalace.

Za kuma a raba tallafin kudi ga wadanda abin ya shafa.

Amma ba a bayar da takamaiman lokacin da za a fara waɗannan tsare-tsaren ba, wanda zai buƙaci albarkatu masu yawa.

Bugu da ƙari, Moroko ta kasance mai zaɓi sosai har ya zuwa yanzu wajen karɓar agajin ƙasashen waje, inda kawai ta amince da samun taimako daga ƙasashe huɗu ciki har da Burtaniya.

Kaɗuwa ta sa wasu sun kasa yin magana

Masu aikin sa-kai na cikin gida sun bayyana min cewa tallafin ba zai tsaya kan gine-gine da kuɗi kawai ba.

Har da lafiyar ƙwaƙwalwar wadanda abin ya shafa, musamman yara kamar waɗanda na yi magana da su.

Ɗaya daga cikin ƙungiyar sa-kai ta kafa kujeru da teburi a cikin wani tanti tana ƙoƙarin taimaka wa matasa shawo kan damuwar da suka shiga ta hanyar zane da rubutu.

"Sun kasance suna zana gidajen da suka ruguje, da dabbobin da suka mutu, sakamakon girgizar ƙasar" In ji wani ma'aikacin jinya mai suna Mohamed Amin a lokacin tattaunawarsa da BBC.

Ya yi tafiya fiye da kilomita 300 daga Rabat babban birnin Morocco, zuwa yankin da girgizar ƙasar ta shafa tare da gungun masu aikin sa-kai, don taimaka wa iyalai masu buƙata.

"Lokacin da muka fara zuwa, yara sun ƙi magana da mu, sun kasance cikin tsoro da rauni sosai," in ji shi.

Sai da suka ɗauki kwanaki da dama kafin suka fara tunkarar abin da suka fuskanta.

Zai ɗauki ƙarin kwanaki da yawa kafin a fara warkewa daga wannan bala'in da ta same su.