You are here: HomeAfricaBBC2023 07 01Article 1795943

BBC Hausa of Saturday, 1 July 2023

Source: BBC

Kotun Ƙolin Amurka ta soke shirin yafe wa ɗalibai bashin karatu

Shugaban Amurka Joe Biden Shugaban Amurka Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya sha alwashin lalubo wata hanyar da zai bi domin yafe bashin da gwamnati ta ba dalibai na karatu, bayan da Kotun Kolin kasar ta soke shirinsa na yafe bashin na sama da Amurkawa miliyan 40.

Hukuncin kotun wanda alkalai 6 suka yi rinjayi 3, ya bata wa al’ummar kasar ta Amurka rai.

Wannan hukunci da kotun kolin ta yi na soke shirin Shugaba Biden na yafe wa daliban bashin da aka ba su na karatu ya haifar da tasgaro ga wani muhimmin alkawari ne da shugaban ya yi a lokacin yakin neman zabensa na yafe bashi.

Ba don hukuncin kotun ba, da Amurkawa sama da miliyan arba’in ne za su ci moriyarsa, inda wasu daga cikinsu suka samu bashin da ya kai dala dubu 10, wasu ma ya kai dala dubu 20.

Da wannan hukuncin Mista Biden bai karaya ba, inda ya yi alkawarin bullo da wasu hanyoyi da zai rage nauyin bashin na karatun gaba da sakandire ko jami’a, ta hanyar amfani da wasu dokokin kasar.

A wani jawabi da ya yi a fadar mulkin kasar, White House Mista Biden ya ce, ya san cewa akwai miliyoyinAmurkawa a kasar, wadanda ba su ji dadi ba kuma gwiwarsu ta yi sanyi, ko ma a ce su dan harzuka. Wanda shi ma ya ji hakan.

Kafin hukuncin daman, an dan sarara da batun yafe bashin tun bayan da wasu gwamnatocin jihohi masu ra’ayin rikau a Amurkar suka shigar da kara, inda suke cewa shugaban kasar ya wuce gona da iri a kan ikon da yake da shi.

Wanda kuma hakan kotun kolin ita ma ta yarda, ta yanke wannan hukunci.

Nan da nan manyan ‘yan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican suka yaba da hukuncin.

shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Kevin McCarthy na Republican da ke hamayya da ta Biden Democrat, ya ce shirin yafe bashin haramtacce ne, kuma yana nufin cewa Amurkawa da ba bashin a kansu ke nan da ba zai zama tilas a kansu ba su biya domin wadanda suka ci bashin ba.

Jumulla dai kusan mutane miliyan 43 ne a Amurka ke da wannan bashi na dalibai a kansu, ko a ce duk cikin manya shida, daya ya ci bashin na akalla karatun gaba da sakandire.

Gwamnatin Biden ta fuskanci shari’a biyu a kan wannan batu, inda a guda daya jihohin ‘yan Republican shida, Nebraska da Missouri da Arkansas da Iowa da Kansas da South Carolina suka kalubalanci shirin.

A daya sharia’r kuma masu kalubalantar suka hada har da wasu dai-daikun mutane biyu da suka ci moriyar bashin na dalibai.

A dukkanin shari’un biyu masu karar sun kafe cewa bangaren zartarwar na gwamnati, ba shi da ikon da zai fito gaba-gadi kawai ya soke wannan bashi.

Daga cikin wadanda suka ci wannan bashi iya wuya akwai Satra Taylor, mai karatu na wucin-gadi, wadda kuma mai fafutuka ce ta wata kungiyar daliban da ke neman a yafe bashin, Young Invincibles, da bashin da ta ci ya kai na dala dubu 103.

Kuma ta gaya wa BBC cewa tana sa ran kudin ya karu domin za ta ci gaba da karatun digirin-digirgir, wato na uku.

Ta ce, iyayenta ba su fito daga gidan attajirai ba, saboda haka ba ta da wani zabi illa ta ci wannan bashi na dalibai domin ta iya kai wa matsayin da za ta ci ta sha ta biya kudin hayar gidan.

Ta ce hukuncin ya bata mata rai sosai, amma ta ce tana da kwarin gwiwa Shugaba Biden zai tabbatar hakarsa ta cimma ruwa, soke wannan bashi ya tabbata.