You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1854005

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Kotu za ta raba gardama kan kujerar gwamnan Kaduna

Isa Ashiru da Gwamnan Kaduna Uba Sani Isa Ashiru da Gwamnan Kaduna Uba Sani

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna za ta yanke hukunci a shari'ar da ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP Isa Ashiru Kudan ya shigar inda yake kalubalantar Sanator Uba Sani na jam'iyyar APC.

Yayin da kowa ne ɓangare ke nuna kwarin-gwiwa na samun nasara a hukuncin da kotun za ta sanar ranar a Alhamis din nan 28 ga watan Satumba 2023, bisa ga dukkan alamu ana zaman kila-wa-kala ne na walau hukuncin ya tabbatar da nasarar ta APC ko kuma akasin hakan.

Tuni aka tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na jihar don kauce wa abkuwar tashin hankali bayan sanar da hukuncin kotun.

Tun da aka fara sauraron karar a farkon watan Yuni na wannan shekara ta 2023 kan zaɓen da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris 2023, dimbin magoya-baya sukan yi dafifi zuwa kotun domin gani da sauraron yadda karar ke gudana.

A lokacin zaman kotun an rika tayar da jijiyar wuya tsakanin lauyoyin ɓangarorin biyu inda kowa ke kokarin tabbatar da hujjojinsa.

Kowa ne ɓangare na nuna ƙwarin gwiwar nasara a shari'ar

Wasu magoya bayan ɗan takarar na jam'iyyar PDP sun sheda wa BBC cewa hujjojin da lauyoyinsu suka bayar su ke ba su kwarin gwiwar cewa su za su yi nasara a shari'ar.

Honorabul Bashir Ibrahim Saka-dadi wanda shi ne jagoran yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan na PDP, ya ce bisa dalilan da suka sa suka je kotu su ne hujjojin da ke hannunsu.

"Kuma mun samu shedu daga hukumar zaɓe da kayayyakin zaɓe din ya tabbatar da mu a zahirin gaskiya abin da muke kuka gaskiya ne sakamakon zaɓe ya nuna mu muka ci zaɓe," in ji shi.

Ya ce fatansu shi ne alkalan da suka zauna shari'ar su tabbatar musu da cewa ɗan takarar tasu, Isa Ashiru Kudan shi ne zababben gwamnan jihar Kaduna.

To sai dai shi ma a nashi ɓangaren wanda ake karar, gwamnan jihar ta Kaduna Sanata Uba Sani ya ce yana da kwarin gwiwar shi zai yi nasara kamar yadda sakataren yaɗa labarai na jam'iyyarsu ta APC, Salisu Tanko Wusono ya sheda wa BBC.

"Mu abin da muka kalla da kuma fatanmu shi ne kotu za ta yanke hukunci shari'ar nan ta ba jam'iyyar APC tare da al'ummar jihar Kaduna da suka taru suka zaɓi jam'iyyar da Mallam Uba Sani bisa dalili guda daya" in ji shi.

"PDP duk zaman da aka yi a kotun nan sun kasa bayar da gamsassun hujjoji cewa an yi musu maguɗi a inda suke cewa an yi musu maguɗin," a cewarsa.

A bisa wannan dalilin ne ya ce suke da imanin kan yadda suka bibiyi shari'ar cewa kotun ba za ta yi wani abu da ya saba wanda suke tsammani na tabbatar musu da nasara ba.

An tsaurara matakan tsaro

Tun a lokacin da aka fara sauraron karar a wata uku da ya gabata an riƙa tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da ke Kaduna to amma a yanzu tsaron ya fi na baya, yayin da ake shirin bayyana sakamakon, inda a wannan karon aka tsaurara matakin musamman a birnin fiye da a baya.

Mukaddashin kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Mansur Hassan ya gaya wa BBC cewa an yi hakan ne domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

Ya ce, rundunar karkashin Kwamishinan 'yan sanda na jihar Musa Yusuf Garba ta samar da wadatattun jami'ai domin tabbatar da kare rayuka da kuma dukiyar al'umma da dukkanin masu ruwa da tsaki a shari'ar.

"Wannan ya haɗa da su kansu masu gabatar da shari'a da lauyoyi da kuma duk wadanda suke da ruwa da tsaki domin mu tabbatar da mun kare duk wani abu da zai zo," in ji kakakin.