You are here: HomeAfricaBBC2021 03 05Article 1197115

BBC Hausa of Friday, 5 March 2021

Source: BBC

Kotu ta dakatar da yin muƙabalar Sheikh Abduljabbar da Malaman Kano

Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara

Wata kotu a jihar Kano da ke araewacin Najeriya ta dakatar da yin muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da malaman Kano da aka shirya yi.

A ranar Juma'a ne Mai Shari'a Muhammad Jibrin na Kotun Majistirate da ke Gidan Murtala, ya yanke hukuncin sakamakon buƙatar da wani lauya mai zaman kansa Barista Ma'aruf Yakasai ya shigar gabanta.

Barista Yakasai dai ya buƙaci a dakatar da gwamnati daga yin muƙabalar ne, saboda hakan ya ci karo da umarnin da kotun ta bayar tun da fari na hana Sheikh Abduljabbar karatu da kuma saka karatukansa a daukacin kafofin yada labaran jihar.

Sai kuma bukatarsa ta biyu da yake son ya shiga cikin waɗanda gwamnatin Kano take ƙara, sai dai ba a amince da wannan ba har sai an sanar da Abuljabbar da kwamishinan ƴan sandan jihar a cewar kotun.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta bi wannan umarni na kotu, inda Kwamishinan Shari'a Barista Musa Lawan ya yabbatar da cewa babu muƙabala a ranar Lahadi mai zuwa.

Lauyan Barista Ma'aruf wato Barista Lukman Auwalu Abdullah ya ce sun ji dadin umarnin kotun.

Ya ƙara da cewa abin da ya sa Barista Ma'aruf ya shiga cikin lamarin shi ne saboda ya tunatar da dukkan ɓangarorin cewa bai kamata a yi muƙabala ba, duba da umarnin kotun na farko na haramta wa Abduljabbar karatu.

A ganinsa yin muƙabalar tamkar an bar shi ya yi karatun ne wanda hakan soke umarnin kotun ne da yi mata rashin biyayya.

Yanzu dai an tsayar da ranar 22 ga wata Maris din da muke ciki don sauraran roƙon da Barista Ma'aruf Yakasai kan dukkan buƙatun.