You are here: HomeAfricaBBC2023 09 05Article 1838624

BBC Hausa of Tuesday, 5 September 2023

Source: BBC

Ko yaya yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ya kasance a jihohin Najeriya?

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Bisa dukkan alamu za a iya cewa yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ya fara tasiri a wasu jihohin Najeriya.

Ƙungiyar ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwana biyu ne domin nuna ɓacn rai game da tsadar rayuwa da ƴan ƙasar suka shiga bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar ta ki halartar zama da gwamnatin tarayya ta kira a ranar Litinin a ƙoƙari da take na dakatar da su shiga yajin aikin da suka fara a yau Talata.

A Abuja, babban birnin Najeriya, an garkame sakatariyar gwamnatin tarayya, amma an buɗe wani sashi na sakatariyar inda ma'aikata suka shiga domin aiki yadda aka saba.

Sai dai an samu ƙarancin fitar ma'aikata idan aka kwatanta kamar na sauran ranakun aiki.

A jihar Kano, rahotanni sun tabbatar da cewa ma'aikata ba su fito ba a Gidan Murtala, wanda ya kasance cibiya da ta kunshi ofisoshi da ma'ikatun gwamnatin jihar Kano.

Har ila yau, wakilin BBC ya ruwaito cewa a can sakatariyar gwamnatin tarayya ma ma'aikata ba su fito ba.

Rahotanni sun bayyana cewa ma'aikatan da ba su wurin aiki ba su suka fi yawa.

Wasu rassan bankuna ma ba su buɗe ba.

Wasu makarantu ma ba bu ɗalibai abin da ke nuna cewa yajin aikin ya fara aiki, inda a kwalejin nazarin harkokin tsafta aka faɗa wa ɗaliban da suka je cewa su koma gida.

"Shigowar mu makaranta kawai sai aka ce mana an tafi yajin aiki, an ce kowa ya tafi gida ba za a yi karatu ba," in ji wani ɗalibin makarantar.

Ita ma wata ɗaliba ta ce "har mun shiga aji mun fara karatu, kawai sai aka ce mu koma gida ba bu karatu. Gaskiya ba mu ji daɗi ba saboda mun kashe kuɗi mun zo makaranta."

Hukumar raba hasken wutar lantarki ta jihar ta Kano (KEDCO) ita ma ta kasance a rufe fayau ba bu ko ma'aikaci, inda aka garkame kofar shiga hukumar.

Sai dai kasuwanni na ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

Ababen hawa ma na yin zirga-zirga sai dai ba kamar kullum ba.

A jihar Legas, harkoki na tafiya yadda aka saba, a cewar wakilin BBC.

Ya ce yawancin ma'aikatu na buɗe, inda kalilan ne kaɗai ba su je aiki ba.

Sai dai ya ce an zuba ƴan sanda a kan hanyoyi, inda suke tsayar da mutane tare da yin bincike.

Rahotanni sun ce ana ci gaba da zirga-zirgar yau da kullum, sai dai ba bu cunkoso.

A can jihar Kaduna ma rahotanni sun bayyana cewa yajin aikin ya fara aiki duk da cewa mutane na ci gaba da harkokinsu.

Mutane na ci gaba da zirga-zirga, inda aka buɗe kasuwanni.

Sai dai bankuna na rufe.

A jihar Adamawa ma yajin aikin ya ɗan samu karɓuwa, saboda mafi yawan ma'aikatun gwamnati na a rufe.

Wani ɗan jarida mai suna Mubarak Aliyu Sabo da muka tattauna da shi, ya bayyana cewa wasu bankuna sun kasance a buɗe ba tare da bin umarnin ƙungiyar ƙwadagon ba.

Sai dai ya ce ƙungiyar ƙwadagon ta fara zagayawa zuwa waɗannan bankuna domin dakatar da kwastomomi shiga tare da tilastawa ma'aikata ficewa.

Ɗan jaridar ya ce makarantu da dama na rufe musamman ma kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar da kuma sauran makarantu, inda ya ce dama yau wasu makatantu suka yi niyyar buɗe wa saboda tafiya hutu da aka yi.

Ya ce a sakatariyar gwamnatin jihar da hukumar bayar da ruwan sha an tilastawa ma'aikata komawa gida bayan zuwa aiki da suka yi.

Sai dai ya ce kasuwanni na ci gaba da gudana a lokacin haɗa wannan labari.

A cewarsa, mutane ma na ci gaba da zirga-zirgarsu ta yau da kulluma kamar ba bu abin da yake faruwa.

"Mutanen gari ba su ma san ana wannan yajin aiki ba, ɓangaren ma'aikata ne kawai abin ya shafa," in ji ɗan jaridar.

Sai dai bisa dukkan alamu yajin aikin bai samu karɓuwa yadda ya kamata ba a jihar Taraba saboda ma'aikatun gwamnati da dama sun kasance a buɗe kuma ma'aikata na gudanar da harkokinsu.

Wani ɗan jarida mai suna Ahmad Ibrahim da muka zanta da shi ya ce duk da cewa ma'aikata sun je aiki, amma akwai ƙarancin ma'aikata.

Ya ce ana ci gaba da zirga-zirga kamar yau da kullum.

Ya ce "kasuwanni da bankuna duka na buɗe, ana gudanar da harkoki."