You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811933

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Ko rushewar yarjejeniyar fitar da hatsi ta Ukraine za ta janyo ƙarancin abinci?

Hoton alama Hoton alama

Dakatar da yarjejeniyar hatsi da Rasha ta yi tsakaninta da Ukraine ta haifar da gagarumar fargabar fuskantar ƙarancin abinci ga ƙasashen Afrika da ke fuskantar fari.

Da yawan masu saka ido na duniya, sun yi mamakin wannan gagarumin matakin da fadar Kremlin ta ɗauka ana dab da fara taro tsakanin Rasha da Ƙasashen Afrika, wanda za a fara a ranar 27 ga watan Yuli a St Petersburg.

Yarjejeniyar da aka sabunta a karo na uku tun bayan fara aikinta a watan Yuli 2022, ta ba da damar wucewar jiragen ruwa a tekun Bahrul Aswad daga tashar jiragen ruwan Odesa da Chornomorsk da Yuzhny/Pivdennyi.

Gwamnatin Kenya ta bayyana matakin na Rasha a matsayin bi-ta-da-ƙulli, ta kuma ce hakan zai shafi ƙasashen gabashin Afrika.

matakin na dakatar da jarjeniyar ya gurgunta shirin samar da abinci na Afrika, ya haifar da fargabar jefa mutane da dama cikin barazanar kamuwa da yunwa da kuma tashin farashi.

Ta yaya hakan zai shafi samar da abinci?

Sama da mutane miliyan 50 ne a ƙasashen, Somalia da Kenya da Ethiopia da kuma Sudan ta Kudu ke cikin matsananciyar buƙatar tallafin abinci, saboda ƙarancin ruwan sama da suka fuskanta na tsawon shekaru.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yarjejeniyar fitar da hatsi ta Ukraine na ba ta damar kai tallafin abinci tan 625,000 zuwa waɗannan ƙasashe.

"Cinikin abinci da takin zamani a tekun Bahrul Aswad ya taimaka wajen daidaita farashin abinci.

Abin takaici ne saboda talakawa da ƙasashen da ke cikin talauci su ne suka fi shan wahala," in ji Ngozi Okonjo-Iweala shugabar hukumar cinikayya ta duniya.

Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce yarjejeniyar ta taimaka wajen rage farashin abinci a duniya da kashi 11.6 cikin ɗari, daga watan Yulin 2022.

Akwai damuwar cewa al'amura za su iya taɓarɓarewa.

"Yanayin kasuwar zai canza nan take. kasancewar kasuwa ko da yaushe na amfani da sabon abu," in ji Dr Constantinos, wani masanin tattalin arziƙi kuma farfesa a ɓangaren tsare-tsare na gwamnati a jami'ar Addis Ababa

"Da zarar an yi wannan sanarwar, masu sayar da hatsi za su ƙara farashinsu, ƙasashe za su ɓoye abinci, kuma su hana fitar da shi."

Hauhawar farashin abinci da tsadar rayuwa sun haddasa mummunar zanga-zanga a Kenya.

Masana tattalin arziƙi sun yi gargaɗi kan yadda lamarin zai iya shafar fannonin tattalin arziƙi masu yawa.

Dr Constantinos ya ce " Ƙasashe za su fuskanci babbar matsala wajen samun alkama da man girki da kuma takin zamani da ake samu daga Rasha, za kuma su fuskanci matsala musamman a ɓangarorin da suka shafi ƴan gudun hijira da kuma waɗanda suka rasa muhallansu a Afirka."

Ko Rasha za ta canza ra'ayi?

Shugaba Putin ya bayyana ƙarara matsayar Moscow kan cewa za ta dawo da yarjejeniyar da zaran ƙasashen Yamma sun cika dukkan buƙatun Rasha da suka haɗa da cire dukkan takunkumai da ci gaba da hada-hadar kuɗaɗe.

Wannan martani ne kan matsin da ƙasar ke fuskanta daga sauran ƙasashen duniya a ƙoƙarin su na shawo kan matsalar.

Masu ruwa da tsaki na duniya, ƙarƙashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya da Tarayyar Turai da kuma wasu ƙasashen Afrika, sun shiga wata tattaunawa da jami'an Rasha.

Suna dai ƙoƙari ne domin ɓullo da mafita da za ta taimaka wajen samar da yalwataccen abinci da kuma tsaro a ɓangaren samar da abincin.

Shin hakan zai shafi goyon bayan da ƙasashen Afirka ke bai wa Rasha?

Kasadar da Rasha ta yi ta dakatar da yarjejeniyar za ta iya lalata alaƙarta da abokan hulɗarta a Afirka.

Za a gudanar da taro tsakanin Rasha da wasu ƙasashen Afirka a birnin St Petersburg, daga ranar Alhamis 27 da Juma'a 28 ga wannan wata na Yuli.

Ƙasashen Afirka 14 sun dogara ga Rasha da Ukraine wajen samun alkama.

Rasha na tallafa wa ƙasashen Libya da Mali da Sudan da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, da Mozambique da sauran wasu sassan Afirka wajen yaƙi da ƴan ta-da-ƙayar-baya da masu iƙirarin jihadi.