You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824803

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Ko rushe-rushen gidaje take adalci ne a Indiya?

Hoton alama Hoton alama

"Sun rushe komai cikin dakiku," in ji Mohammad Saud a cikin hawaye, yana tsaye gaban wani babban tarin tarkacen.

Shi da kaninsa Nawab Sheikh suna kallon shagunansu da aka rusa da ke gundumar Nuh a jihar Haryana da ke arewacin Indiya. A yayin da yake magana da BBC a ranar Asabar.

"Muna da shaguna 15 da muka gina a kan filin mu. Muna da dukkan takardun filayen amma 'yan sanda suka dage da cewa gine-ginen ba bisa ka'ida aka yi su ba," in ji Mista Saud.

Gine-ginen su na daga cikin daruruwan shaguna da gidaje da hukumomin gundumar suka rushe sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a makon da ya gabata a Nuh, gundumar da musulmi suka fi yawa, wadda ke cikin matalautan yankin babban birnin kasar Indiya wanda ya hada da Delhi da yankinsa.

‘Yan sanda sun ce an fara arangama tsakanin mabiya addinin Hindu da musulmi ne bayan wani tattaki karkashin jagorancin wata kungiyar Hindu masu tsatsauran ra’ayi da duwatsu a lokacin da ta wuce ta Nuh.

Yayin da labarai ke yaduwa, tashin hankali ta kuma barke a Gurugram, kusa da Delhi.

An kashe mutane shida a Nuh da Gurugram yayin da masu tarzoma suka kona shaguna da ababen hawa da kuma wani masallaci.

Baya wasu kwanaki, sai aka zo da motar rusau aka fara rushe shaguna da gidaje da dama a gundumar Nuh wanda ake zargin an gina su ba bisa ka'ida ba. Matakin dai ya tsaya ne bayan kwanaki hudu, a ranar Litinin kuma sai babbar kotun jihar da kan ta ta bayar da sanarwa ga gwamnati.

“Wannan a bayyane yake, an yi amfani da matsalolin doka da oda wajen aiwatar da rusau ba tare da wani umarni da kuma bin hanyar da doka ta tanadar ba,” in ji kotun.

Kungiyoyin farar hula da jam'iyyun adawa sun ce an yi ta samun yawan tashe-tashen hankula da kalaman kyama ga musulmi tun shekara ta 2014, lokacin da jam'iyyar BJP mai ra'ayin kishin addinin Hindu karkashin jagorancin Firayim Minista Narendra Modi ta hau kan karagar mulki.

A Jihohin da BJP ke mulki kamar Uttar Pradesh, Madhya Pradesh da Assam, rushe gidajen mutanen da ake zargi da aikata laifuka ya zama ruwan dare. Dalilin da aka ambata game da rusan shi ne gine-gine ba bisa ka'ida aka yi su ba amma masana shari'a suna kokwanton hakan.

Su ma manyan Ministocin wadannan Jihohin sun sha alakanta rushe gidajen da shagunan da irin tsauraran matakan da gwamnatinsu ta dauka kan aikata laifuka.

Yayin da wadanda abin ya shafa suka hada da iyalan mabiya addinin Hindu, shugabannin adawa da kuma masu fafutuka da dama sun ce an fi daukar matakin ne kan musulmi, musamman bayan tashin hankalin addini ko zanga-zanga.

A Nuh, jami'ai sun ba da amsoshi masu cin karo da juna lokacin da aka tambaye su dalilin rushe-rushen. Alkalin gundumar Dhirendra Khadgata ya shaida wa BBC Hindi cewa gine-ginen da ba bisa ka'ida aka yi su ba ne kawai ake rushewa. Amma Vinesh Singh, jami'in tsare-tsare na gundumar, ya ce hukumomi sun rusa gidajen da daga ciki ne akayi ta jefe-jefe ".

Masu suka sun ce wadannan rushe-rushen na da matukar muni yayin da suke bar mutane da dama marasa laifi, ciki har da yara da rashin matsunguni.

"Rushe gidan ko shagon wani ba bisa ka'ida ba wani nau'i ne na hukunci na gama-gari," in ji masanin kimiyyar siyasa Asim Ali. "

Masana shari'a sun yarda cewa zartar da hukunci nan take da rashin mutuntaka ne kuma ba bisa ka'ida ba.

"Ta yaya gwamnati za ta ruguje gidaje da dama ba tare da wani bincike ba kuma da sanin gaskiyar lamarin"

Mai shari'a Madan Lokur, wani tsohon alkalin kotun koli ya yi nuni da cewa, a cewar rahotanni, “ba a bai wa masu gidajen sanarwar da ya dace ko kuma lokacin da ya kamata su kwashe kayan su daga gidajensu ba kuma dan lokaci su nemi wani gidan da zasu iya komawa.

Ba a yarda da lalata kayan farar hula da gangan ba a ƙarƙashin kowace doka, in ji Shadan Farasat, lauyan Kotun Koli. "Idan kuna so ku tuhumi wani da laifin tashin hankali, ana buƙatar kama shi sai a gurfanar da shi a gaban kuliya - bubu inda aka ce hakan nan a rusa gidan mutum a cikin kwana daya ba.

Mai shari’a Lokur ya ce hukumomi ba su da ikon rusa gine-ginen da ba bisa ka’ida ba sai dai an ba su dama ta hanyar doka. Dole ne a ba wa mai gidan sanarwa kuma a ba shi damar biyan tara ko shigar da ƙara. Ko a lokacin, hukumomi na da zabin ruguza sassan da aka gina kawai wanda ya saba wa doka. Idan tsarin gaba ɗaya ya sabawa doka, dole ne hukumomi su ba da bayanin "dalili" ga mai ginin kafin rushe shi. “An bayar da rahoton cewa ana gudanar da aikin rusa gaba daya ba bisa ka’ida ba, kuma hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa baki daya,” in ji shi.

A Nuhu, 'yan sanda sun ce sun aika da sanarwa ga wadanda ake zargi da aikata laifin, amma iyalai da dama sun shaida wa BBC cewa ba su samu gargadi ba. Wasu kuma sun yi ikirarin cewa ba su ma a cikin gidajensu a lokacin da rikicin ya faru amma an hukunta su.

Musaib, mai shekaru 20, ya kasa daina kuka yayin da ya ke kallon yadda hukumomi ke rusa shagonsa na mako guda, wanda ya gina da ajiyar mahaifinsa.

"Yaya zan sake gina rayuwa na yanzu?" Ya tambaya.

“Iyali mutum 10 ne suke rayuwa saboda wannan shagon, an tilasta mana fitowa kan tituna yanzu,” inji shi.

Wasu kuma na fargabar cewa raba gari zai iya wargaza zaman lafiya a Nuh, inda mabiya addinin Hindu da Musulmai suke rayu cikin jituwa shekaru da yawa.

Yayin da an dakatar da rusau a halin yanzu, wasu musulmi mazauna yankin sun ce ba su da kwanciyar hankali.

"A kullum ana zaluntar mu, ina za mu je idan irin haka ta sake faruwa?" Malam Sheikh yace.

Amma ba kowa ne ya yarda cewa hukumomi sun yi kuskure ba.

“Gwamnati ta yi abin da ya dace, ya kamata a koya wa wadannan ‘yan tarzoma darasi,” in ji Ashok Kumar, wanda ya raka abokansa kallon yadda ake ruguza gidajen.