You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798598

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

Ko bashin karatu na gwamnatin Najeriya zai magance matsalar ilimi?

Wasu taliban Najeriya Wasu taliban Najeriya

Gidan Esther Abu ya cika da sowa bayan sun ji labarin sabuwar dokar da za ta bai wa 'ya'yan talakawa damar karɓar rancen kuɗi don yin karatun jami'a.

Ƙaramar 'yar Abu, mai shekara 10 da ɗoriya, za ta kammala sakandare a wata mai kamawa.

Tana son yin karatu a fannin nazarin kwamfuta, amma ta sani sarai cewa mahaifiyarta, wadda bazawara ce, da kyar take iya saya musu abinci ballantana ta iya ɗaukar nauyin karatunta da albashin aikin sharar titi.

Babbar 'yar tata ta gama sakandare shekara biyu da suka gabata kuma ta fara aikin gyaran gashi domin tallafa wa dangin nata da ke zaune a yankin Mararaba na birnin Abuja.

"Ina da burin zama likita tun ina yarinya," a cewar Eunice mai shekara 21.

Dukkansu yanzu suna da dama, kodayake dai 'yar kaɗan ce, ta cimma burikansu yayin da gwamnati ta ce za ta samar da rance na biyan kuɗin makarantar. Sai dai kuma an ɗiga ayoyin tambaya iri-iri game da tsarin rancen.

Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki matakai daban-daban tun bayan hawansa mulki a ƙarshen watan Mayu - ciki har da cire tallafin man fetur, da karya darajar naira, da korar gwamnan babban banki, da sake hafsoshin tsaro.

Tsawon shekaru, gwamnati ta ƙi ƙara kuɗin makaranta domin ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa su yi karatun sakamakon talauci da kuma ƙarancin ilimi a faɗin ƙasar.

Yayin da ɗaliban aikin likita a Jami'ar Legas ke biyan N25,000 (dala 26) a zangon karatu, takwarorinsu na Jami'ar Ghana da ke birnin Accra na biyan cedi 3,500 (dala 308).

Sai dai gwamnati ba ta iya cike gurbin da ƙarancin kuɗin makarantar ta haifar ba a jami'o'i, inda akasarinsu ke cikin halin lalacewa da cika maƙil da ɗalibai da kuma ƙarancin albashi ga malamai.

A albashi na tsaka-tsaki, farfesa a Najeriya na ɗaukar albashin da bai wuce naira 500,000 ba a wata (dala 725), yayin da ƙaramin malamin jami'a ke samun N160,000.

Wannan yanayi ne ya jawo yajin aiki iri-iri da suka haifar da rufe jami'o'in na tsawon lokaci a shekarar da ta gabata - karo na tara ke nan cikin shekara 13.

Yawaitar shiga yajin aiki ya sanya mutane da dama ba su da ƙwarin gwiwa kan jami'o'in gwamnatin ƙasar, wasu na shiga na 'yan kasuwa masu tsadar gaske ko kuma su fice daga ƙasar.

Bijiro da rancen na nufin Shugaba Tinubu ya bai wa jami'o'i damar ƙara kudin makaranta, wanda gwamnati ke fargabar 'ya'yan talakawa ba za su iya biya ba.

Tinubu ya ce tsarin zai "faɗaɗa damar samun ilimi ga dukkan 'yan Najeriya ba tare da nuna bambanci ba".

Za a dinga cirar kashi 10 cikin 100 na albashin wanda ya karɓi bashin a kowane wata, shekara biyu bayan sun kammala hidimar ƙasa.

"Amma me zai faru idan suka gama makarantar kuma ba su samu aiki ba?" kamar yadda Mrs Abu ta tambaya cikin sanyayyar murya.

Irin wannan tambayar ake ta yi a dukkan sassan Najeriya tun daga ranar da aka bayyana sabon tsarin.

A binciken da aka gudanar a 2020, ɗaya cikin kowane mutum uku da ke neman aiki bai samu ba a Najeriya, sannan kuma miliyoyi na yin aikin da bai kai kimar abin da suka karanta ba kamar na gyaran gashi.

"Na san aƙalla mutum 200 da suka gama makaranta kuma suka koma ƙauyenmu suka ci gaba da noma saboda babu aikin yi," in ji Ayuba Mayah, ɗalibi a Kwalejin Ilimi ta Zuba, Abuja.

Ya ce ba zai karɓi bashin ba saboda ya guje wa alaƙaƙai a lokacin da yake fafutikar neman aiki.

Sadiya Aminu da Mercy Sunday, da ke karanta fannin tattalin arziki a kwaleji ɗaya, sun aminta cewa samun aiki bayan karatu ne fargabarsu game da rancen.

"Iyayena ba su taɓa tunanin wani bashi ba lokacin da suka tura ni makaranta, za su san yadda za a yi su biya kuɗin," a cewar Ms Mercy wadda iyayenta manoma ne.

Duk da cewa Tinubu ya yi alƙawarin rage adadin marasa aikin yi da rabi cikin shekara uku ta hanyar ƙirƙirar miliyoyin ayyuka, dokar ba ta ce komai ba game da waɗanda suka kasa biyan bashin saboda rashin aiki.

Sai dai kuma, waɗanda suke zaman kansu na cikin haɗarin ɗauri a gidan yari na shekara biyu ko kuma tarar kashi 10 na ribarsu idan suka ƙi biyan bashin.

An buƙaci masu neman bashin su gabatar da masu tsaya musu aƙalla biyu:

  • babban ma'aikacin gwamnati


  • lauya mai ƙwarewar aiki ta shekara 10


  • jami'i a ɓangaren shari'a ko alƙali


  • Duk da cewa ba lallai ne da yawan 'yan Najeriya su iya cimma waɗannan ƙa'idojin ba, ko da sun yi hakan babu tabbas za su samu rancen saboda sai akwai kuɗi a ƙasa.

    Shugaban ƙungiyar malaman jami'a ya ce tsarin ba "mai yiwuwa ba ne", yana mai cewa kashi 90 na ɗaliban ba za su iya cika ƙa'idojin ba.

    Farfesa Mudashiru Mohammed na jami'ar jiha a Legas yana ganin an saka ƙa'idojin don tabbatar da cewa duk wanda ya karɓa ya biya a ƙasar da mutane da yawa ke kallon kuɗin gwamnati a matsayin na banza.

    Akasarin iyayen ɗaliban na fama da tsadar kuɗin sufuri da ya riga ya hauhawa, ga kuma farashin kayan abinci da shi ma ya haye a kwanan nan.

    Yanzu za su ƙara da kuɗin makaranta da ya tashi a wasu jami'o'in - waɗanda da ma suke ta hanƙoron ƙarawa tun daga shekarar da ta wuce - da kusan ninki biyu.

    An ce bashin na biyan kuɗin makaranta ne kawai, ban da sauran abubuwa kamar kuɗin ɗaki da na abinci, waɗanda sun ninninka na karatu yawa.

    "Idan ba za su biya duka ba to mene ne amfanin bashin? Wane ne zai sayi litattafai, ya biya kuɗin ɗaki, ya sayi abinci," kamar yadda Mrs Abu ke tambaya.

    Ba wannan ne karon farko da Najeriya ke ɓullo da tsarin rance ba a fannin ilimi - irin wannan tsari da gwamnatin soja ta fito da shi a 1972 bai ɗore ba saboda mutane sun ƙi biya bashin, in ji Farfesa Mudashiru.

    "Zai fi kyau 'ya'yana su koyi sana'a ko ƙananan ayyuka sama da su shiga jami'a kuma su wuce gidan yari daga nan," in ji Mrs Abu.