You are here: HomeAfricaBBC2023 08 07Article 1820222

BBC Hausa of Monday, 7 August 2023

Source: BBC

Ko Salah zai koma Saudiyya?

Mohamed Salah Mohamed Salah

A yayin da ake ta rade-radin yiwuwar komawar Mohamed Salah Saudiyya, wakilinsa ya bayyana cewa dan wasan na da matukar kishin Liverpool a zuciyarsa.

Jaridar Al-Riyadiah ta Saudiyya ta ce Al-Ittihad ta tuntubi dan wasan kuma ta yi masa tayin kwantiragin shekara biyu kan albashin fan miliyan 155 ga Salah, inda za ta biya Liverpool fan miliyan 52.

Salah, mai shekara 31 ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta shekaru uku a bazarar da ta wuce wadda za ta kare a watan Yunin 2025.

Tuni Liverpool ta sayar da 'yan wasan tsakiya Fabinho da Jordan Henderson ga Al-Ittihad da El-Ettifaq a wannan bazarar, yayin da Roberto Firmino ya koma Al-Ahli bayan karewar kwantiraginsa a Anfield.

Dan wasan na Masar ya lashe kofin Zakarun Turai da Premier League da FA Cup da League Cup, da kuma Uefa Super Cup a Liverpool.

Gasar kwallon kafa ta Saudi Pro League ta dauki manyan 'yan kwallon kafa tun bayan da Cristiano Ronaldo da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya koma gasar a watan Janairu daga Manchester United.

Wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or na yanzu, Karim Benzema, da Fabinho, da tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea N'Golo Kante, da tsohon dan wasan Celtic Jota duk sun koma Al-Ittihad, wanda tsohon kocin Tottenham da Wolves Nuno Espirito Santo ke jagoranta.

Har wa yau, 'yan wasa irin su Riyad Mahrez, Sergej Milinkovic-Savic, Sadio Mane, Ruben Neves, da Allan Saint-Maximin duk sun koma taka leda a Saudiyya.