You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716407

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Ko Real za ta kara rage tazarar maki tsakani da Barca a La Liga?

Yan wasan Real Madrid Yan wasan Real Madrid

Ranar Asabar za a ci gaba da wasannin mako na 22 a gasar La Liga, inda Real Madrid za ta ziyarci Osasuna.

Ranar 2 ga watan Oktoban 2022 kungiyoyin suka tashi 1-1 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu.

Real Madrid wadda take ta biyu a teburin La Liga na fatan rage tazarar maki takwas zuwa biyar idan ta yi nasara a gidan Osasuna ranar Asabar.

Barcelona wadda ke jan ragama, wadda ta tashi 2-2 da Manchester United a wasan neman gurbin Europa 'yan 16 za ta kara da Cadiz a Nou Camp ranar Lahadi.

Tun farko Barcelona ta bai wa Real tazarar maki 11, baya da ta Santiago Bernabu ta je Morocco buga kofin duniya na zakarun nahiyoyi.

Real wadda ta lashe Fifa World Club Cup ranar Asabar a Morocco da cin Al Hilal 5-2 ta kammala atisayen tunkarar Osasuna.

Dan wasa Hazard da Mendy sun motsa jiki a rufaffen daki, yayin da Toni Kroos bai halarci atisayen ba, sakamakon ciwon ciki.

Wasannin mako na 22 da za a fara a La Liga:

Juma'a 18 ga watan Janairu

  • Girona da Almeria Match details


  • Asabar 18 ga watan Janairu

  • Real Sociedad da Celta de Vigo


  • Real Betis da Real Valladolid


  • Real Mallorca da Villarreal


  • Osasuna da Real Madrid


  • Lahadi 19 ga watan Janairu

  • Elche da RCD Espanyol


  • Rayo Vallecano da Sevilla


  • Atletico Madrid da Athletic Bilbao


  • FC Barcelona da Cadiz


  • Getafe da Valencia