You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816562

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Ko Mbappe zai koma Chelsea?

Kylian Mbappe Kylian Mbappe

Rahotanni sun ce kungiyar Paris St-Germain ta bai wa Kylian Mbappe wa'adin sabunta kwantiragi a ranar 1 ga watan Agusta ko kuma ya bar kungiyar.

Ana rade-radin cewa dan wasan na Faransa, mai shekara 24, ya amince ya koma Real Madrid a kakar wasa mai zuwa a kyauta idan kwantiraginsa a PSG ya kare.

Mbappe na damar barin PSG a kakar bana - ko dai a matsayin aro ko kuma a kan kwangilar dindindin, wanda ta hakan ne PSG za ta iya samun kudi a kansa.

Sai kuma yanzu ga Chelsea da Barcelona na nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan.

A cewar wata majiya, mamallakin Chelsea, Todd Boehly, yana son Mbappe amma yana fuskantar gogayya daga Barcelona inda kungiyoyin biyu ke da niyyar bayar da ‘yan wasa da kuma tsabar kudi.