You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716422

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Ko Arsenal za ta koma mataki na daya a Premier kuwa?

Kocin Arsenal Mikel Arteta Kocin Arsenal Mikel Arteta

Ranar Asabar za a ci gaba da wasan mako na 24 a gasar Premier League, inda za a yi fafatawa takwas.

Daga ciki Arsenal za ta ziyarci Aston Villa a wasa na biyu da za su kara a Premier League a bana.

Ranar 31 ga watan Agusta Arsenal ta doke Aston Villa 2-1 a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

Arsenal tana mataki na biyu a teburi da maki 51 iri daya da na Manchester City ta daya da tazarar rarar kwallaye.

Ranar Laraba City ta yi nasara a kan Arsenal da ci 3-1 a kwantan wasan mako na 12 a Premier da suka buga a Emirates.

Gunners ta ci karo da koma baya a wasa na uku a jere a bana kenan, bayan da Everton ta doke ta 1-0 a Goodison Park da 1-1 da ta tashi a gida da Brentford.

Mikel Arteta ya karbi aikin horar da Arsenal ranar 20 ga watan Disambar 2019, wanda ya maye gurbin Unai Emery.

Kawo yanzu ya ja ragamar wasa 118 a Premier League da cin 65 da canjaras 19 aka doke shi 34.

Karkashin Arteta Arsenal ta ci kwallo 195 aka zura mata 129 tun daga lokacin da ya karbi aiki a kuma wasannin Premier League.

Arsenal wadda City ta fitar da ita daga FA Cup na bana, ba ta kai bantenta a Carabao Cup da za a yi wasan karshe tsakanin Newcastle da Manchester United ba.

Kofin da Arsenal ke fatan daukar a kakar nan shi ne na Europa League, wadda ta kai zagayen 'yan 16 da kuma na Premier League.