You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829132

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

Klopp na fatan a soke jan katin da aka bai wa Mac Allister

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp da Alexis Mac Allister Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp da Alexis Mac Allister

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce yana sa ran za a soke jan katin da aka bai wa Alexis Mac Allister a wasan Premier League da Bournemouth ranar Asabar.

Mai shekara 24 dan kasar Argentina, wanda ya koma Anfield daga Brighton a bana kan fam miliyan 58, an kore shi daga karawar da Liverpool ta ci 3-1.

Za a dakatar da Mac Allister wasa uku, bayan da ya taka kafar Ryan Christie daga nan aka ba shi jan katin.

Bournemouth ta fara cin kwallo ta hannun Antoine Semenyo a minti uku da take leda.

Liverpool ta farke ta hannun Luis Diaz a minti na 27, sai Mohammed Salah ya kara na biyu, bayan da ya barar da bugun fenariti tun farko.

Kungiyar Anfield tana da ci 2-1, sannan aka kori Mac Allister daga fafatawar.

Diogo Jota ne ya ci na uku da ya bai wa Liverpool damar hada maki ukun da take bukata a fafatawar mako na biyu a Premier League