You are here: HomeAfricaBBC2021 05 24Article 1269142

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Kimanin mutum 70 sun jikkata a gobarar da ta ta shi a Kano

Hatsarin ya faru ne a jihar Kano Hatsarin ya faru ne a jihar Kano

Hukumomi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun tabbar da jikkatar gwamman mutane a wata gobara da ta faru a wani gidan mai da ke Unguwar Sharada a Jihar.

Cikin wata tattaunawa da manema labarai kwamishin ayyuka na Jihar Alhaji Garba Idriss Unguwar Rimi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya na cewalaifun na mahukuntan gidan man ne.

"Kowa ya sani doka ta haramta sauke mai da tsakar rana musamman a irin wannan yanayi da Kano ke ciki na matsanancin zafi, wanda kuma hakan ne ya yi sanadiyyar tashin wannan gobara.

"Wannan gobara ta rutsa da mutum 43 na gari, sai kuma jami'anmu 8 da suke je aikin kashe gobarar, wadanda bayan an kashe ta farko wani ma'aikacin gidan man ya bude wani tanki gobara ta biyu ta kara ta shi ta rutsa da su," in ji Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano.

Sai dai rahotanni na cewa adadin wadanda suka jikkatan ya zarce wanda hukumomin suka zayyana.

Da yake kan babbar hanya gidan man yake, lamarin ya rutsa da gwamman mutane da ke kan hanyarsu ta zuwa inda suka nufa, sai kuma 'yan kallo da suka ciki inda gobarar ta faru.

An dai ta kwashe mutane ana karasawa da su babban asibitin Mutala Muhammad da ke tsakiyar birnin na Kano.

Daya daga jikin wadanda suka tsira daga gobarar da yake kwance a asibitin ya shaida wa gidan rediyon Freedom cewa, yana cikin adaidaita sahu zaizai tafi unguwa kawai sai yaji kamar an kwara masa wani abu a bayansa.

"Bayana da duwawuna da bayan hannuwana duk sun kone, tafin kafafuwa na ma duk a kone suke," in ji wani da gobarar ta rutsa da shi.

Shi ko wani Musbahu Rabi'u Yaro da ke Unguwar Sharada Rinji cewa ya yi, ya dawo daga lebiranci sai ya ji karar fashewar abu, kan ya ankara wutar ta cimmasa, inda ta kona kafafunsa da kansa da kuma yuwansa.

Wata mata da aka kirata domin ta zo wajen danta da abin ya rutsa da shi ta ce, ta dauki hanya za ta Karamar Hukumar Rano kawai aka sanar mata da wannan ibtila'i.

"Shi ne yake daukar nauyinmu, da aka kirani na dauka konewar kadance, amma daga baya naga ya kone sosai, ko magana baya iya yi," in ji matar.

Nura Abdulkadir Maigida shi ne jami'in yada labarai na hukumar kashe gobara na tarayya reshen Jihar Kano ya ce suna bincike domin su tabbatar da musabbabin wannan gobara domin kiyayen kara faruwarta a nan gaba.