You are here: HomeAfricaBBC2021 05 31Article 1274527

BBC Hausa of Monday, 31 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Lukaku, Xhaka, Pochettino, Dybala, Niguez, Wijnaldum

Romelo Lukaku, dan wasan Inter Milan a Italiya Romelo Lukaku, dan wasan Inter Milan a Italiya

Chelsea a shirye ta ke ta sake daukan dan wasan gaba na Inter Milan Romelu Lukaku kafin kakar wasa mai zuwa, kuma kungiyarsa a shirye ta ke a yi ma ta tayi saboda tana fuskantar kalubalen kudi. (Mail)

Paris St-Germain ma sun sanar ba su da niyyar kyale kocinsu Mauricio Pochettino ya sauya sheka, duk da ana cewa Real Madrid da Tottenham na bukatar sa. (Mirror)

Tottenham na son dauka Antonio Conte a matsayin sabon kocin kungiyar tare da tsohon shugaban sashen wasanni na Juventus Fabio Paratici. (Sport Italia via Express)

Dan wasan tsakiya na Arsenal Granit Xhaka mai shekara 28 ya ce ya ji dadi sabon kocin Roma Jose Mourinho na bukatarsa, amma ya fi son ya ci gaba da jan zarensa a Gunners. (Blick via Goal)

Dan wasan gaba na Argentina Paulo Dybala zai tsawaita zamansa a Juventus har ma ya fara tattaunawa da sabon koci Massimiliano Allegri, wanda shi ma ya zaku ya fara aiki da dan wasan mai shekara 27. (Goal)

Dan wasan tsakiya na Atletico Madrid Saul Niguez, mai shekara 26 zai bukaci a ba shi damar komawa Manchester United, amma Juventus da Paris St-Germain ma na sha'awar sayen dan wasan. (Mirror via Star)

Dan wasan baya na Chelsea, Thiago Silva zai so ya ci gaba da zama a kungiyar na karin kakar wasa daya, saboda yadda ya taimaka wa kungiyar lashe gasar Zakarun Turai. (Evening Standard)

Serge Aurier, dan wasan baya na Tottenham da Ivory Coast mai shekara 28 ya sanar da zai bar kungiyar zuwa Paris St-Germain ko AC Milan saboda sha'awar da su ka nuna. (L'Equipe - in French)