You are here: HomeAfricaBBC2021 04 24Article 1241392

BBC Hausa of Saturday, 24 April 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Konate, Messi, Cristiano Ronaldo, King, Willock

Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus

Liverpool ta cimma yarjejeniya da RB Leipzig a kan dan baya na kasar Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 21, wanda sharadin sayensa daga kungiyar ta gasar Bundesliga shi ne biyan fam miliyan 34. (Jaridar Fabrizio Romano)

Shugaban Barcelona Joan Laporta na shirya yarjejeniyar shekara uku da kungiyar za ta bai wa Lionel Messi, a kokarin da take yi na shawo kan dan wasan na Argentina mai shekara 33 ya ci gaba da zama a kungiyar. (Jaridar ESPN).

Dan wasan gaba na Juventus da kasar Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, na matukar sha'awar komawa Manchester United a bazaran nan. (Jaridar Gazetta dello Sport daga Metro)

Arsenal ta damu ganin cewa za ta iya rasa gwani Martin Odegaard dan kasar Norway mai shekara 22, wanda yake zaman aro a kungiyar daga Real Madrid, sakamakon janyewa daga gasar Turai ta Super League. (Jaridar Sun)

Barcelona na kokarin dawo da dan wasan tsakiya dan Faransa Kays Ruiz-Atil kungiyar, kasancewar kwantiragin dan wasan mai shekara 18 zai kare da Paris St-Germain a karshen kakar da ake ciki. (Jaridar Mundo Deportivo)

Mai tsaron ragar Manchester United na uku Lee Grant, mai shekara 38, zai bar kungiyar a bazaran nan saboda Golan dan Ingila na ganin kungiyar ta saba alkawarinta na ba shi sabon kwantiragi. (Jaridar Mail)

Ana sa ran shugaban Manchester United mai barin-gado Ed Woodwardzai zabi wanda zai gaje shi kafin ya bar Old Trafford. (Jaridar Manchester Evening News)

Newcastle na bukatar biyan Arsenal kusan fam miliyan 20 domin rike dan wasan tsakiya dan Ingila Joe Willock wanda yanzu yake zaman aro a kungiyar, ya zama nata na dindindin. (Jaridar Telegraph)

Kungiyoyin Premier daban-daban da suka hada da Manchester United da abokiyar hamayyarta Manchester City na sa ido sosai kan dan wasan tsakiya na Aston Villa, dan Ingila asalin Najeriya Carney Chukwuemeka, mai shekara 17. (Jaridar Guardian)

Real Madrid na sha'awar sayen dan bayan Manchester City dan kasar Portugal Pedro Porro, mai shekara 21, wanda yanzu yake zaman aro a Sporting Lisbon. (Jaridar AS)

Dan wasan gaba na Everton dan kasar Norway Josh King na tattaunawa da kungiyar Galatasaray ta Turkiyya kuma bias ga dukkan alamu dan wasan mai shekara 29 zai bar kungiyar a bazaran nan. (Jaridar Football Insider)

Mai kungiyar Leeds United Andrea Radrizzani na fatan ganin kociyan kungiyar Marcelo Bielsa will extend his contract at Elland Road before the end of this season. (L'Equipe - in French)