You are here: HomeAfricaBBC2021 04 12Article 1230901

BBC Hausa of Monday, 12 April 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Fellaini, Kane, Salah, Klopp, Thauvin, Cavani, Soumare, Torres

Mohamed Salah, dan wasan Liverpool Mohamed Salah, dan wasan Liverpool

Paris St-Germain ta tuntubi wakilan Mohamed Salah domin soma tattaunawa game da yunkurin daukar dan wasan na Liverpool da Masar mai shekara 28 a bazara. (Telefoot on Twitter - in French)

Kocin PSG Mauricio Pochettino ya tuntubi dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 27, a kan yiwuwar sake hadewarsu tare a babban birnin Faransa. (Telefoot on Twitter - in French)

Leicester City na gaban Manchester United da Tottenham a fafutukar da suke yi ta daukar dan wasan tsakiyar Faransa Boubakary Soumare, mai shekara 22, daga Lille. (Star)

Kocin Tottenham Hotspur Jose Mourinho yana shirin dauko dan wasan tsakiyar Belgium Marouane Fellaini. Dan wasan mai shekara 33, wanda ya murza leda a karkashin jagorancin kocin dan kasar Portugal a Manchester United, yana kungiyar Shandong Luneng ta kasar China tun da ya bar Old Trafford a watan Fabrairun 2019.

Bayern Munich za ta yi yunkurin daukar kocin Liverpool Jurgen Klopp a bazara idan Hansi Flick ya bar kungiyar domin zama kocin Jamus. (90mins)

Sai dai shugaban Bayern Herbert Hainer, ya ce ya yi "matukar gamsuwa cewa" Flick zai ci gaba da zama a Allianz Arena. (Sky Sport Germany, via Goal)

Manchester United ta "matsu" ta dauki dan wasan Villarreal da Sifaniya Pau Torres, mai shekara 24, wanda Bayern Munich da Real Madrid suke zawarci. (AS, via Team Talk)

Crystal Palace ta mayar da hankalinta kan dan wasan Marseille Florian Thauvin, mai shekara 28, a yayin da ta bayyana karara cewa zai yi wahala ta iya daukar dan wasan Senegal mai shekara 23 Ismaila Sarr daga Watford a bazara. Sai dai tuni Thauvin, hdan kasar Faransa, ya soma tattaunawa da AC Milan. (Sun)

Za a fuskanci kalubale kafin Edinson Cavani ya bar Manchester United a bazara saboda ce-ce-ku-cen da ke cikin kudin darajar dan wasan na Uruguay wadanda suka kai £2m. Ana hasashen cewa dan wasan mai shekara 34 yana son tafiya Boca Juniors. (Mirror)

West Ham na son daukar golan Senegal Seny Dieng, mai shekara 26 daga Queens Park Rangers. (Sun)

AC Milan ba za ta sayar da dan wasan gaba Rafael Leao, mai shekara 21, a kan kasa da euro 50m ba. A baya kungiyoyi irin su Everton da Juventus sun so su dauki dan wasan. (Calciomercato - in Italian)

Leicester City na dab da kammala daukar matashin golan Ingila mai shekara 16 Brad Young daga Hartlepool. (Sun)