You are here: HomeAfricaBBC2021 03 30Article 1219441

BBC Hausa of Tuesday, 30 March 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Ana rububin Sergio Aguero, Sabitzer, Menino,

Kociyan Paris St-Germain Mauricio Pochettino da darektan wasanni na kungiyar Leonardo na aiki ba kakkautawa domin ganin sun dauko Sergio Aguero mai shekara 32 dan wasan gaba na Argentina, da zai bar Manchester City da zaran wa'adinsa ya kare a karshen bazara. (Todo Fichajes)

Sai dai kuma ana ganin Barcelona, ce za ta yi nasara wajen dauke dan wasan da ya dauki kofin Premier hudu, wanda kuma ake cewa Real Madrid da Juventus ma na harinsa (Manchester Evening News)

Manchester United, da Liverpool da kuma Tottenham na fafutukar sayen dan wasan tsakiya na Austria Marcel Sabitzer, mai shekara 27, daga RB Leipzig. (Bild, via Sun)

A shirye Everton ta ke ta saurari tayi daga duk wata kungiya da ke son sayen dan bayanta Yerry Mina. Za ta sayar da dan wasan ne dan Colombia mai shekara 26 domin samun kudin da za ta sayi dan wasan baya na Napoli Kalidou Koulibaly, dan Senegal mai shekara 29. (Football Insider)

Manchester City ta ce ba ta da niyyar daukar dan bayan Bayern Munich David Alaba, duk da rade-radin da ake yadawa cewa za ta dauki dan wasan mai shekara 28, wanda zai bar zakarun na Jamus a lokacin bazara. (Manchester Evening News)

To amma kuma an ambato Chelsea da Paris St-Germain a matsayin daya daga cikin kungiyoyin da Alaba, dan Austrian zai tafi, bayan da wakilinsa Pini Zahavi ya musanta maganar da ake yi cewa Real Madrid da Barcelona ne kadai kungiyoyin da ke son daukar dan wasan mai shekara 28. (Diario AS, via Mail)

Kungiyar David Beckham, Inter Miami, ta Amurka wadda Phil Neville, ke horarwa na fafutuka da abokiyar hamayyarta ta DC United wajen daukar tsohon dan wasan Ingila, da Liverpool da kuma Chelsea Daniel Sturridge, mai shekara 31, wand aba shi da kungiya tun lokacin da ya bar Trabzonspor ta Turkiyya a watan Maris na 2020. (Mirror)

Barcelona ta yi wa dan wasan tsakiya na Liverpool Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, tayin yarjejeniyar shekara uku. Dan wasan na Holland zai bar Anfield a karshen wannan kakar. (Mundo Deportivo )

Juventus ta bi sahun Tottenham, da Chelsea da Atletico Madrid a kokarin daukar dan wasan tsakiya dan Brazil Gabriel Menino, mai shekara 20, wanda kila ya bar Palmeiras a kudin da bai gaza fan miliyan 13 ba, saboda matsalar kudin da kungiyar ke ciki. (Mundo Deportivo, via Team Talk)

Dan wasan baya na Faransa Malang Sarr, mai shekara 22, zai koma Chelsea a karshen zamansa na aro a Porto a karshen kakar nan, kasancewar gaba daya kungiyar da da dan wasan bas u amince da zaman nasa ya kasance na dindindin ba. (Record, via Sport Witness)

Arsenal ta zama kungiya ta baya bayan nan da ke sha'awar daukar dan wasan gaba na Fiorentina Dusan Vlahovic, mai shekara 21, inda ta bi layin su Tottenham, da AC Milan, da RB Leipzig da Roma da kuma Atletico Madrid wajen neman dan kasar ta Serbia. (Calcio Mercato - in Italian)