You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218202

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: bbc.com

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Kane, Dembele, Dybala, Pogba, Lloris, Bellerin

Juventus tana son sanya dan wasan Argentina mai shekara 27 Paulo Dybala, wanda kwangilarsa za ta kare a watan Yunin 2022, a cikin musayar da take son yi domin daukar 'yan wasa da dama, ciki har da dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 28. (Football Italia)

Tsohon dan wasan Tottenham Jermain Defoe ya yi amannar cewa dole dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 27, ya bar Spurs idan yana son lashe kofuna. (Talksport)

Barcelona tana son tsawaita kwangilar dan wasan gaban Faransa mai shekara 23 Ousmane Dembele kafin kwangilarsa ta yanzu ta kare a 2022. (Mundo Deportivo)

Manchester United ta gaza daukar Dembele a bazarar da ta wuce amma har yanzu tana ci gaba da son daukar dan wasan kuma tana tuntubar wakilansa. (Sport)

Juventus tana son sanya dan wasan Argentina mai shekara 27 Paulo Dybala, wanda kwangilarsa za ta kare a watan Yunin 2022, a cikin musayar da take son yi domin daukar 'yan wasa da dama, ciki har da dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 28. (Football Italia)

Zai yi wahala golan Faransa Hugo Lloris, mai shekara 34, iya bar Tottenham a bazarar nan, duk da cewa kwangilarsa za ta kare a karshen bazarar 2022. (Football London)

Manchester United ta soma tattaunawa da AC Milan a kan yadda kungiyar ta Italiya za ta sayi dan wasan Portugal mai shekara 22 Diogo Dalot daga matakin aronsa da take yi a halin yanzu. (Metro)

Liverpool za ta gwammace mika £15m domin dauko golan Turkiyya Ugurcan Cakir daga Trabzonspor, a yayin da RB Leipzig da Sevilla su ma suke son dan wasan mai shekara 24. (Express)

Tsohon dan wasan da ke tsaron bayan Arsenal Bacary Sagna ya ce ba zai "yi mamaki ba" idan dan wasan Sifaniya Hector Bellerin, mai shekara 26, ya bar Gunners. (Goal)

Serb Aleksandar Kolarov, mai shekara 35, zai iya barin Inter Milan a karshen kakar wasan da muke ciki, kuma Bologna na daya daga cikin kungiyoyi biyar da ke sha'awar daukar tsohon dan wasan na Manchester City. (Tuttosport - in Italian)

Dan wasan Real Madrid da Jamsu Toni Kroos, mai shekara 31, yana shirin yin ritaya daga buga kwallo a kasashen duniya bayan kammala gasar European Championships a bazara. (Marca)

Join our Newsletter