You are here: HomeAfricaBBC2021 06 01Article 1275439

BBC Hausa of Tuesday, 1 June 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ronaldo da Sterling da Kane da Grealish, Ramos da Roberto

Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus

Manchester United na fatan sake cimma yarjejeniya da ɗan wasan gaba a Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, a wannan kakar. (Express)

Manchester City na iya sayar da ɗan wasanta Raheem Sterling, mai shekara 26, da Benjamin Mendy na Faransa, da ɗan wasan Spain Aymeric Laporte, domin samun kuɗaɗen dauko ɗan wasan Tottenham Harry Kane, mai shekara 27, da mai bugawa Aston Villa Jack Grealish. (Goal)

Manchester United ta kuma nuna zawarcinta a kan Kane da Grealish, yayin da ƙungiyoyi biyu ke shirin shiga fafatawa kan ɗan wasan West Ham asalin ƙasar Ingila mai shekaru 22 Declan Rice. (Mirror)

Pep Guardiola da Manchester City na duba yiwuwar miƙa tayinsu ga ɗan wasan Real Madrid da Spain Sergio Ramos, mai shekara 35, kwangilar shekara biyu, idan yarjejeniyarsa ta ƙare a wannan kakar. (ESPN)

Manchester City na kuma ɗokin ganin ta dauko ɗan wasan tsakiya Sergi Roberto, mai shekara 29, daga Barcelona. (Sport)

Chelsea da AC Milan sun cimma yarjejeniya kan ɗan wasan Ingila mai tsare mata baya, Fikayo Tomori bayan kammala zamansa na aro. (Sport Witness)

Leicester City ta yi zarra a rububin cimma yarjejeniya da ɗan wasan Celtic, Odsonne Edouard. (Football Insider)

Newcastle ta zaƙu ta dauko aron ɗan wasan Chelsea Tammy Abraham, da mai bugawa Scotland tsakiya Billy Gilmour, mai shekaru 19. (Northern Echo)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp na cikin shiri yayin da ƴan wasansa tara za su bar ƙungiyar a wannan kaka, ciki akwai Xherdan Shaqiri da Divock Oirgi ɗan Belgium. (Star)

Barcelona ta bukaci ɗan wasan Brazil Philippe Coutinho mai shekaru 27 ya koma Liverpool domin cike gibin sauran kuɗaɗen da kulob din ke binta daga cinikin ƴan wasa a 2018. (AS - in Spanish)

Chelsea da Manchester United sun nuna a shirye suke su gana da ɗan wasan da Real Madrid ke neman £70m a kansa wato Raphael Varane, ɗan Faransa, kuma kowanne na nuna zai ninka kuɗin. (Defensa Central - in Spanish)

Ɗan wasan Bayern Munich da Poland Robert Lewandowski, yaƙi bayyana abin da yake ciki yayin da ƙungiyoyi irin su Chelsea da Barcelona da Real Madrid ke nuna kwaɗayinsu a kansa. (Canal+ via Metro)

AC Milan na son dauko ɗan wasan Chelsea asalin Faransa Olivier Giroud, idan kwangilarsa ta ƙare a ƙarshen watan Yuni. (Goal)

Everton ta zaƙu ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan Chelsea Pedro, mai shekara 33, daga Roma. (Calciomercato)

Tsohon ɗan wasan Leicester City da kuma koci Kevin Phillips na ganin ƙungiyar ba ta da ƙarfin hana ɗan wasan Belgium Youri Tielemans, koma wa Liverpool bayan sun gaza samun nasara a zakarun Turai. (Football Insider)

Ɗan wasan Arsenal da France, Matteo Guendouzi, a shirye yake ya koma Marseille idan aka cimma daidaituwa tsakani. (L'Equipe via Mirror)

Southampton da Celtic sun nuna zawarcinsu a kan mai tsaron ragar Newcastle Freddie Woodman, mai shekara 24. (Chronicle Live)

Leeds United ta cire ranta akan ɗan wasan Liverpool da Wales Harry Wilson. (Football Insider)

Ɗan wasan Wolves dan asalin Portugal Ruben Vinagre, ya nuna sha'awar koma wa Sporting Lisbon. (Record - subscription required)

Sporting na kuma iya cimma yarjejeniya da ɗan wasan Manchester City Yangel Herrera, mai shekara 23, wanda ya yi zaman aro a Granada a kakar da ta gabata. (A Bola - in Portuguese)

Lazio ta ambato tsohon kocin Chelsea Maurizio Sarri, mai 62 a matsayin zaɓinta na farko, yayin da suke son maye gurbin kocinsu imone Inzaghi, ɗan shekara 45. (Corriere Dello Sport)

Wakilin ɗan wasan Inter Milan asalin Morocco Achraf Hakimi, 22, da ɗan wasan Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23, na cewa suna tattauna farashin ƴan wasan yayinda ƙungiyar ke shirin zabtare kasafinta. (Mail)