You are here: HomeAfricaBBC2021 04 19Article 1236433

BBC Hausa of Monday, 19 April 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Messi da Mbappe da Ibrahimovic, Kean da Palmieri

Lionel Messi, dan wasan Barcelona Lionel Messi, dan wasan Barcelona

Har yanzu Barcelona ba tayi Lionel Messi tayin ci gaba da zama a ƙungiyar ba, ƙwantiragin ɗan wasan Argentinan mai shekara 33 zai ƙare a ƙarshen wannan kaka.(Marca)

Tattaunawa tsakanin Barcelona da ɗan wasan gaban Faransa, Ousmane Dembele mai shekara 23 kan sabon ƙwangila da ƙungiyar ta yi nisa, yarjejeniyar da yake kai a yanzu ba zata ƙare ba sai shekara ta 2022. (Sport - in Spanish)

Kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino na fatan Kyale Mbappe ɗan Faransa mai shekara 22 zai amince da sabon yarjejniyar da kulob din ke fatan gabatarsa masa. (Goal)

Alexandre Lacazetta ya ce yanke shawarar sanya hannu a sabon yarjejeniya da Arsenal ba daga gareshi kawai take ba, kwangilar da ya cimma da ƙungiyar a yanzu ba zata kare ba sai karshen 2022. (Mirror)

Matakin Moise Kean mai shekara 21 na komawa Everton bayan kammala zaman aro a PSG abin mamakine a cewar ɗan uwansa Giovanni. (Tuttosport, via Football Italia)

Kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann ya jadada cewa bai tattauna da Bayern Munich kan maye gurbin Hansi Flick a matsayin sabon kocinsu ba. (Goal)

Inter Milan na zawarci ɗauko ɗan ƙasar Italiya, Emerson Palmieri mai shekara 26 daga Chelsea. (Todofichajes - in Spanish)

Mai bugawa ƙasar Poland kuma ɗanw asan gaba a Arsenal Wojciech Szczesny, mai shekara 31, ba zai bar Juventus domin koma wa Tottenham ba a wannan kakar. (Goal)

Darakta a ƙungiyar AC Milan, Ricky Massara ya ce yana sa ran ƙungiyar ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 39, kuma yana da yaƙinin cewa mai tsaron ragar Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 22, da mai buga tsakiya a Turkiyya Hakan Calhanoglu, mai shekara 27, za su sanya hannu kan sabon kwantiragi da ƙungiyar ta Seria A. (DAZN, via Football Italia)