You are here: HomeAfricaBBC2021 06 07Article 1280254

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mbappe, Haaland, Ward-Prowse, Odegaard, Neves, Laporte, Giroud

Kyliam Mbappe, dan wasan PSG da tawaggar Faransa Kyliam Mbappe, dan wasan PSG da tawaggar Faransa

Shugaban Paris St-Germain Nasser Al-Khelaifi ya ce ba za su sayar da dan kwallon tawagar Faransa, Kylian Mbappe mai shekara 22 ba. (AS - in Spanish)

Bayan da ba ta samu daukar Buendia ba Arsenal na son sayen dan wasan Norway, Martin Odegaard, ya sake buga mata tamaula dan kwallon Real Madrid, ko dai wasannin aro ko kuma a sayar mata da shi. (Football London)

Barcelona na son sake zawarcin dan wasan Manchester City Aymeric Laporte, za kuma ta iya musaya da Sergi Roberto, cikin kunshin yarjejeniya. (Sport - in Spanish)

Dan kwallon tawagar Faransa Olivier Giroud, zai iya komawa AC Milan, da taka leda duk da cewar Chelsea ta sanar da tsawaita kwantiragin kaka daya tare da shi a makon jiya. (Goal)

Barcelona ta zabi kin kara kudin farashi da ta yi wa Georginio Wijnaldum, bayan da Paris St-Germain ta kara kudin da Barca ta taya tun farko. Dan wasan tawagar Netherlands wanda yarjejeniyarsa zai kare a Liverpool, a karshen watan nan, zai koma PSG kan kwantiragin kaka uku. (Fabrizio Romano, Twitter)

Juventus za ta nemi dan kwallon da Barcelona ke son dauka dan kasar Netherlands, Memphis Depay, wanda ake cewar zai bar Lyon a karshen watan nan da yarjejeniyarsa za ta cika, (Mundo Deportivo)

Kocin Atletico Madrid Diego Simeone na daf da saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar kungiyar kaka biyu zuwa karshen 2024 - ya kuma bukaci da a dauko masa dan kwallon Argentina Lautaro Martinez daga Inter Milan. (AS - in Spanish)

Real Betis na ci gaba da tattaunawa da dan kwallon Paraguay, Fabian Balbuena, wanda kwantiraginsa ke daf da karewa a West Ham. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tottenham za ta tabbatar da nada tsohon kocin Juventus Fabio Paratici cikin makon nan, bayan da batun daukar tsohon kocin Juve da kuma Inter Milan Antonio Conte ta bi ruwa. (Mirror)

Lazio za ta bai wa tsohon kocin Juventus da kuma Chelsea Maurizio Sarri, aikin horar da kungiyar cikin makon nan. (Corriere dello Sport - in Italian)