You are here: HomeAfricaBBC2021 05 25Article 1270258

BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Karim Benzema ya ci wa Real Madrid kwallo 30 a bana

Karim Benzema ya ci kwallo 30 a Real Madrid a kakar bana, kuma karo na uku yana yin wannan bajintar.

Real Madrid ta buga wasan karshe a La Liga bana ranar Lahadi, inda ta doke Villareal da ci 2-1, kuma a karawar ce Benzema ya ci kwallo daya na kuma 30 jumulla.

Wannan ne karo na biyu da ya zura 30 a raga a kaker 2018/19, yayin da ya ci 32 a kakar 2011/12.

Irin wannan kwazon da Benzema ya yi bana a Real Marid ya sa tawagar kwallon kafar Faransa ta gayyace shi gasar cin kofin nahiyar Turai da za a fara cikin watan Yuni.

Cikin kwallayen da ya zura a raga a bana sun hada da 23 a La Liga da guda shida a Champions League da kuma daya a Spanish Super Cup.

Kaka bakwai a jere Benzema na cin kwallaye da yawa a Real Madrid, yana kuma cikin wadanda ke kan gaba a bayar da kwallo a zura a raga mai tara a bana.

Cikin kaka 12 da yake a Real Madrid, Benzema yana cikin zakakuren 'yan kwallon Real Madrid da suka kafa tarihi da yawa, suka kuma kare martabarta a fannin tamaula a duniya.

Yana cikin na 10 a jerin wadanda suka buga wa Real wasanni da yawa, ya kuma yi kan-kan-kan da Michel a wannan bajintar.

Shi ne na biyar a jerin 'yan wasan da suka ci wa Real kwallaye mai 279 a tarihi, kuma na hudu a kungiyar a jerin wadanda suka zazzaga kwallaye a La Liga mai 192 a raga.