You are here: HomeAfricaBBC2023 06 26Article 1793024

BBC Hausa of Monday, 26 June 2023

Source: BBC

Karen da ke takara da mutum 101 don zama magajin gari a Kanada

Hoton alama Hoton alama

Nan gaba kaɗan mazauna birnin Toronto na ƙasar Kanada za su zaɓi sabon magajin gari bayan wanda yake kan muƙamin ya sauka saboda ɓullar labarin neman mata da yake yi.

Sai dai akwai masu zawarcin kujerar tasa da yawa, inda 'yan takara 102 ke fafatawa (shi ne adadin mafi yawa a tarihi) - cikinsu har da kare.

Sunan karen dai Molly.

Karen ɗan shekara shida da mai shi Toby Heaps, na yi wa mutane alƙawarin "daƙile amfani da gishiri" a kan titunan birnin lokacin hunturu.

Yawan amfani da gishiri a kan tituna lokacin sanyi, in ji Mista Heaps, zai shafi faratan karnuka kamar na Molly.

Haka kuma, yana son ya rage yawan mutanen da ba sa iya samun matsugunni, da kuma ƙara wa masu kuɗi haraji, da hana amfani da na'urorin da ke amfani da makamashi mai gurɓata muhalli a gidaje kamar na ɗumama ɗaki.

Idan ya yi nasara, ya ce zai ayyana Molly a matsayin magajin gari na karramawa a karon farko.

"Ina ganin mahukuntan garin nan za su fi ɗaukar matakan da suka dace idan akwai kare a cikinsu," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Wannan zaɓen cike-gurbi na farko a tarihin Toronto tun bayan haɗewar gundumomi guda shida zuwa abin da ake kira "ƙasaitaccen gari" (mega city) shekara 25 a baya.

An fara takara ne bayan John Tory ya sauka daga muƙaminsa, bayan ya shafe shekara takwas a kan mulki.

Hawan Mista Tory muƙamin magajin gari a 2014, ya zama abin murna bayan mulkin Rob Ford, wanda ya bayyana ƙarara cewa yana shan hodar kokino (koken) lokacin da yake mulki.

Sai dai kuma an sha sukar Mista Tory saboda ƙarancin manufofin inganta rayuwa ga birnin na Toronto, da kuma amincewa da rashin daidaito a ɗaya daga cikin biranen duniya mafi tsadar rayuwa.

Duk da haka, an zaɓi Tory har karo uku, nasarar baya-bayan nan ita ce a watan Oktoban 2022.

'Yan takara ƙalilan ne suka ƙalubalance shi a lokacin.

Wata maƙala da aka wallafa a mujallar Toronto Star ta bankaɗo cewa mutumin mai shekara 68 ya yi soyayya da wata 'yar shekara 31 a lokacin annobar korona duk da yake yana da aure. Ya ajiye muƙamin nasa 'yan awanni bayan wallafa labarin.

Kasancewar babu shi a wannan zaɓen, fafatawar za ta zama ta "dukkan 'yan takara," in ji Farfesa Nelson Wiseman na Jami'ar Toronto.

"Bambanci tsakanin wannan lokacin da wancan shi ne ba mu san wanda zai yi nasara ba," a cewar farfesan.

Abin da kawai ake buƙata daga wani ɗan Toronto kafin ya shiga takara shi ne ya biya dalar Kanada 250 da kuma sa hannun mutum 25.

Saɓanin sauran manyan birane a nahiyar Arewacin Amurka kamar New York, Los Angeles, Chicago, ba a ƙarƙashin tutar wata jam'iyya ake takarar ba.

Ƙwararru sun faɗa wa BBC cewa ganin yadda da ma ake fama da rashin fitowar masu kaɗa ƙuri'a a Toronto, da yawan 'yan takarar na neman a san su ne kawai.

Babbar 'yar takara a zaɓen ita ce Olivia Chow, wadda take aikin gwamnati tun 1992. Akasarin masu adawa da ita tsofaffin kansiloli ne da kuma masu ci, waɗanda kuma sanannu ne.

Amma bambancin da aka samu a wannan karon tsakanin 'yan takara kamar na kare Molly da kuma mai shekara 18 da bai daɗe da kammala makaranta ba - na nuna yadda kawuna suka rarrabu a birnin, a cewar Mista Chapple.

Toronto mai ƙunshe da mazauna kusan miliyan uku, cikinsu har da sabbi da kuma 'yan ci-rani, shi ne birni na uku mafi girma a nahiyar Arewacin Amurka, wanda kuma ake yawan bayyana shi a matsayin birni mafi bambancin al'umma a duniya.

Samuwar waɗannan mutane masu asali da kuma al'adu daban-daban a birnin tasa ake da fahimta iri daban-daban game da yadda Toronto ya kasance.

Yayin da ake da 'yan takara da yawa, Mista Heaps - mai mallakar kare Molly - ya ce ya san ba lallai ne ya zama magajin garin Toronto ba. Ya yanke shawarar shiga takarar ce bayan tattaunawa da ɗansa mai shekara bakwai.

"Na ce e, amma ka san akwai yiwuwar ba za mu yi nasara ba. Ya za ka ji ke nan?" a cewar Mista Heaps.

"Ya ce 'zan ji ba daɗi, raina zai ɓaci, amma zan yi ji daɗi ka gwada sa'arka'."

"Hakan ma ya yi min daidai."