You are here: HomeAfricaBBC2022 10 12Article 1641401

BBC Hausa of Wednesday, 12 October 2022

Source: BBC

'Karbar na goro a hannun direbobin manyan mota a Najeriya ya zame mana masifa'

Hoton alama Hoton alama

Wani matuƙin babbar motar dakon kaya a Najeriya ya koka kan yadda cin hanci yake yin mummunan tasiri a kan aikinsa da yake yi na jigila tsakanin arewa da kudancin ƙasar. Malam Bello Haruna, ɗan asalin garin Potiskum a jihar Yobe da ake arewa maso gabashin Najeriya, ya ce a ƙalla yakan kashe naira 170,000 a duk jigila ɗaya da zai yi don kai kaya. Direban babban motar ya faɗa wa BBC hakan ne bayan wallafa neman jin ra’ayin mutane a wani shirin tattara labarai na musamman gabanin zaɓukan 2023. Bello, wanda ya aiko da labarinsa kan yadda batun cin hanci ya yi ƙamari a Najeriya, ya ce ba a madafun ikon da ke can sama kawai ake cin hanci ba, “A ƙasa ma ƙananan jami’ai suna yin son ransu.” Mutumin ya ce baya ga barazanar tsaro da suke cin karo da ita a kan hanyoyin da suke bi ɗin, ya yi zargin cewa jami’an tsaro kuma kan dinga tatike su da karɓar na goro ba tare kuma da sun samar musu wata kariya daga komai ba. Bello dai kan ɗauki kayan gwari ne ko dankalin Hausa ko shanu daga wasu jihohin arewa zuwa kudu a babbar mota, kuma ya ce yakan wuce shingayen bincike masu yawa wanda kowanne sai an tsayar da shi. “Sau da dama idan na tashi daga Sakkwato zuwa Fatakwal wallahi duk checkpoint din da na zo sai sojoji sun karɓi a ƙalla naira 5,000 ko fiye da haka. “Don haka a tafiya ɗaya wata rana sai direba ya kashe sama da N150,000,” ya ce. Bello ya ce yakan bi hanyoyin Fatakwal da Enugu da Aba daga ko dai Kano ko Sakkwato kusan sau uku a duk wata ɗaya. Duk da cewa ba Bello ba ne kawai direban da ya yi wannan ƙorafi, a bayyane yake cewa karbar cin hanci daga jami’ai daga hannun ƴan ƙasa abu ne da aka shaida ya zama ruwan dare kuma ba ya cikin tsarin Najeriya. Ƴan zaman banza Bello ya ce baya ga jami’an sojoji da ba sa karɓar abin da ya gaza N5,000, jami’an ƴan sanda ma kan tayar da su su karɓi nasu kason, “sai dai su ko ƴar naira 200 zuwa 500 ka ba su ba sa rainawa,” ya ce. “Wani abin takaicin kuma baya ga jami’ai mukan haɗu da matasa zauna gari banza da ake kira eriya boyis musamman a yankin kudanci. “Su kuma waɗannan inda suke tsayawa gaba kaɗan ne da sojojin kuma su ma dole mu ba su kudi, in ba haka ba su yi wa rayuwarmu barazana. “Abin haushin kuma sojojin da muka bai wa kudin suna kallon abin da ake yi don tazarar babu nisa amma babu wata hoɓɓasa da za su yi don ba mu tsaro,” Bello ya faɗa. Bello ya ce akwai wani lokaci da irin wadannan zauna gari banza suka tare su a kusa da shingen binciken sojoji don karbar na goro sai suka ba su haƙuri cewa sai wani jiƙon, “wallahi sai suka far mana da duka har suka karya yaron motata,” in ji shi. Direban ya kuma koka kan yadda a ƙoƙarin karɓar na goron nan da jami’an ke yi yake jawo cunkoson ababen hawa a kan hanyoyin inda ake sa su ɓata lokaci sosai. “Ga hada go slow da suke yi ga kuma cin zarafin duk wanda bai ba su kudin ba, ba sa karbar duk wani uzuri daga wurin direba in har ka ce su yi haƙuri ba ka da kuɗi to kuwa za ka fuskanci wulaƙanci da tozarci, abin dai ba daɗin ji. “A wasu shingayen za ka ga sojoji uku har zuwa biyar ma a wasu lokutan,” ya ce. Mummunan tasiri Wani zai yi mamakin to ta ina direbobin ke samun kudin da Bello ya ambata cewa suna kashewa a duk tafiya ɗaya? Ya ce dama ana gaya wa ainihin mai mota cewa ga fa yanayin da ake ciki don haka shi zai bayar da waɗannan kuɗaɗe. “Shi ya sa aikin namu duk wahala ta fi samun yawa.” A nazarin da muka yi, mun fahimci cewa yawanci shi mai mota zai fanshe kuɗaɗen da direba ya kashe ɗin ne a jikin masu kayan da za a kai wa kudu ɗin, daga nan su ma dole sai sun ƙara farashin kayayyakin nasu don su fanshe. Kenan hakan zai iya yin tasiri wajen ƙarin hauhawar farashi. Malam Bello ya ce idan har ana son kawar da cin hanci a Najeriya, to kowa sai ya saka hannu an yaƙi abin a tare, “don ba a sama ba ne kawai, lamarin ya munana a harkokinmu na yau da kullum ma,” ya ce.g