You are here: HomeAfricaBBC2021 05 24Article 1268746

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Kano Pillars ta koma ta daya a Firimiyar Najeriya

Kano Pillars ta tashi 1-1 a gidan Katsina United Kano Pillars ta tashi 1-1 a gidan Katsina United

Kano Pillars ta tashi 1-1 a gidan Katsina United a wasa na 22 a gasar Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Lahadi.

Kyaftin, Rabiu Ali ne ya ci wa Pillars kwallo a minti na 26 da fara wasa, inda Katsina mai masaukin baki ta farke ta hannun Ahmed Rasheed kafin hutu.

Da wannan sakamakon Pillars ta dare kan teburin Firimiyar Najeriya da maki 41, bayan wasa 22.

>Sai a ranar Litinin ake sa ran Akwa United mai maki 40 wadda take ta biyu mai wasa 21 za ta karbi bakuncin Enugu Rangers.

Cikin wasa takwas da aka fafata ranar Lahadi karawar mako na 22, ba kungiyar waje da ta je ta yi nasara.

Yayin da kungiyoyi hudu daga waje suka yi canjaras, haka ma na gida hudun ne suka raba maki, inda aka zura kwallo 21 a raga.

Ga sakamakon wasannin mako na 22 agasar ta Firimiyar Najeriya:

  • Katsina United 1-1 Kano Pillars


  • Nasarawa United 3-1 Heartland


  • Plateau United 4-1 Wikki


  • Rivers United 0-0 Abia Warriors


  • Jigawa Golden Stars 1-1 Dakkada FC


  • FC Ifeanyiubah 1-0 Sunshine Stars


  • MFM 1-0 Lobi Stars


  • Adamawa United 3-3 Warri Wolves


Ranar Litinin 24 ga watan Mayu:

  • Akwa United da Enugu Rangers