You are here: HomeAfricaBBC2021 06 07Article 1280221

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

Kano Pillars ta hau kan teburi, bayan doke Enyimba

Nasarar da Pillars ta yi a kan Enyimba ta hada maki 48 kenan a karawa 25 a gasar kakar nan Nasarar da Pillars ta yi a kan Enyimba ta hada maki 48 kenan a karawa 25 a gasar kakar nan

Kano Pillars ta yi nasara a kan Enyimba International da ci 2-1 a wasan mako na 25 a gasar Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Lahadi a Kaduna.

Enyimba ce ta fara zura kwallo a ragar Pillars ta hannun Victor Mbaoma, kuma haka suka je hutu da ci 1-0.

Bayan da suka koma wasa na biyu bayan hutu kyaftin Rabiu Ali ya farke a bugun fenariti, kuma kwallo na 10 da ya ci a kakar bana kenan.

Kasa da minti 15 a tashi daga wasan Pillars ta kara na biyu ta hannun Ifeanyi Eze da hakan ya bai wa kungiyar Kano maki ukun da take bukata.

Da wannan sakamakon Pillars wadda take bani in baka a jan ragamar teburin Firimiyar Najeriya a bana da Akwa United, yanzu ta koma ta daya a makon nan.

Nasarar da Pillars ta yi a kan Enyimba ta hada maki 48 kenan a karawa 25 a gasar kakar nan.