You are here: HomeAfricaBBC2023 06 03Article 1779236

BBC Hausa of Saturday, 3 June 2023

Source: BBC

Kane ya taya Pochettino murnar karbar aikin kocin Chelsea

Harry Kane da Mauricio Pochettino Harry Kane da Mauricio Pochettino

Harry Kane ya taya Mauricio Pochettino murna da yi masa fatan alheri, bayan da Chelsea ta sanar da nada shi sabon kocinta.

Pochettino ya ja ragamar Tottenham har ya kai su zuwa wasan karshe a Champions League a 2019.

Haka kuma ya dora kungiyar cikin fitattu a gasar Premier League, inda Tottenham ta kare a cikin 'yan hudun farko karo biyu a jere daga baya ta kore shi a 2019.

Kyaftin din Tottenham yana New York a karshen makon nan, domin sanar da zuba jari da zai yi a OxeFit, don yin hadaka da kamfaninsa.

Pochettino, wanda ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyu da cewar za a iya tsawaita masa ita idan ya taka rawar gani, ya maye gurbin kocin rikon kwarya Frank Lampard.

Chelsea ta kammala kakar bana a mataki na 12 a Premier League, kaka mafi muni da ta yi rashin kokari tun bayan 1994.