You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809524

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

Kane ba zai stsawaita kwantaraginsa ba, Sadio Mane zai koma Al-Nassr

Harry Kane Harry Kane

Harry Kane, mai shekaru 29, ba zai sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da Tottenham ba, sannan za a iya komawa Bayern Munich. (Times - subscription required)

Dan wasan Netherlands Arnaut Danjuma, mai shekaru 26, ya shirya koma wa Everton a matsayin aro daga Villarreal. (Sky Sports)

Aston Villa ta amince da yarjejeniyar Bayer Leverkusen kan Moussa Diaby na Faransa, mai shekaru 24. (Birmingham Live)

Tottenham ta gano cewa za ta iya maye gurbin dan wasan Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekaru 27, wanda kuma ya ke tattaunawa a kan komawa Atletico Madrid da dan tsakiyar Aston Villa Douglas Luiz da kuma dan tsakiyar Ingila Conor Gallagher. (Mail)

West Ham ta kusa samun nasara a rige-rigen da ake yi kan dan wasan Manchester City Carlos Borges, wanda Borussia Dortmund da Eintracht Frankfurt ke son dauka, bayan da ta taya shi a kan fam miliyan 14. (Guardian)

Manchester City na duba yiwuwar daukar dan wasan Lyon Bradley Barcola, mai shekaru 20, a matsayin wanda zai maye gurbin Riyad Mahrez. (90min)

Paris St-Germain ma na sanya ido a kan Barcolan. (Le Parisien - in French)

Manchester United ta shirya mika tayinta na farko ga Atalanta a kan dan wasan Denmark Rasmus Hojlund, mai shekaru 20, wanda PSG ma ke son ɗauka. (Fabrizio Romano)

Dan gaban Bayern Munich ɗan ƙasar Senegal Sadio Mane, mai shekaru 31, ya amince da yarjejeniyar komawa Al-Nassr. (90min)

An yi wa mai horar da kungiyar Fulham dan kasar Portugal Marco Silva, mai shekaru 46 tayin fam miliyan 40 kan yarjejeniyar shekara biyu don zama kocin kungiyar Al-Ahli. (Sky Sports)

Al-Ahli na harin ɗan tsakiyar Arsenal ɗan kasar Ghana Thomas Partey, mai shekaru 30. (Mail)