You are here: HomeAfricaBBC2023 02 23Article 1720085

BBC Hausa of Thursday, 23 February 2023

Source: BBC

Kamfanin da kwamfyuta ke tashin mutum daga aiki don ya huta

Hoton alama Hoton alama

Sakamakon halin tsanani da ma’aikata kan shiga a wuraren aikinsu inda suke shafe tsawon lokaci, bayan lokacin da ya kamata su tashi daga aiki su koma gida, kamfanin harkokin fasahar zamani na SoftGrid Computers a Indiya ya ƙirƙiro wata manhaja da ke rufe kwamfuyatar ma’aikaci da zarar lokacin tashinsa na ƙa’ida ya yi.

Tanvi Khandelwal, ma’aikaciya ce mai shekara 21 wadda tana daga cikin mutum 40 da kamfanin da ke birnin Indore a jihar Madhya Pradesh na ƙasar ya ɗauka aiki kwanan nan.

Ta tuna yadda wannan tsari ya ba ta mamaki, lokacin tana tsakar aiki sai kawai ta ga wani rubutu ja ya fito mata a kwamfyuta yana gargaɗinta cewa kwamfyutar za ta rufe kanta nan da minti 10 saboda lokacin tashinki aiki ya yi. ‘’Don Allah ki tafi gida.’’

Ms Khandelwal, wadda take aiki a sashen kula da harkokin ma’aikata na kamfanin ta fahimci cewa an saka wannan manhaja domin ta riƙa tashi daga aiki a kan ƙa’ida, inda kwamfyutar ma’aikaci ke rufe kanta.

Babbar jami’ar gudanarwa ta kamfanin, Shweta Shukla, ta ce wannan tsari da suka yi na daga cikin ƙoƙarinsu na taimaka wa ma’aikata ta yadda za su riƙa jin daɗin aikinsu ba tare da sun gaji ko wahala ba.

Da take bayyana dalilinsu na ƙirƙiro manhajar ta ce, ‘’Annobar korona ta rikita lokaci da kwanakin ayyukanmu, inda muka riƙa aiki na tsawon lokaci. Na riƙa fama kan yadda zan samu lokacin kula da dana,’’ in ji ta.

Sauran abokan aikinta a kamfanin suma suna fama da wannan ƙalubale a lokacin.

Daga nan ne suka buƙaci wani abokin aikinsu ya ƙirƙiro mahnajar da za ta riƙa fitowa da rubutu na gargaɗi a kwamfyutar ma’aikaci minti goma kafin lokacin tashin ma’aikacin cewa kwamfyutar za ta rufe kanta idan lokaci ya yi.

Wata shida da ya gabata aka sanya wannan mahnaja a dukkanin kwamfyutar ma’aikatan kamfanin.

Ms Shukla ta ce,’’ Mun sanya manhajar ne a ƙarshen mako domin muna so mu shammaci kowa, mu ba su mamaki. Lokacin da rubutun ya fito kwatsam a kwamfyutoci sai wasu suka yi cirko-cirko, wasu suka dauƙa saƙo ne na bogi wasu kuma suka ɗauka an yi musu kutse ne a kwamfyuta.’’

Shugabar ta ce sun zaɓi wnnan tsari na fitowar wannan rubutu ne na gargaɗi, maimakon rubuta wata wasiƙa ta faɗakar da ma’aikata kan tashi a lokacin da ya kamata, domin a cewarta wannan tsari ya fi ƙayatarwa da burgewa.

Ma’aikatan sun yaba da tsarin da cewa taƙaitacciyar faɗakarwa ce da ke ankarar da ma’aikaci da ya bar ofis ya nufi gida domin ya huta.

Ma’aikaciya Khandelwal ta ce wannan wani abu ne da ya bambanta da inda take aiki a baya, inda ba a son mutum ya tashi daga aiki da wuri , hasali ma har so ake mutum ya ƙara lokaci a wurin aikin.

Ta sanya bayanin wannan tsari a shafinta na LinkedIn kusan mako ɗaya da ya wuce, inda ta ƙara da bayanin cewa, ‘’ aiki a irin wannan tsari ba ka buƙatar wani abu na ƙarfafa gwiwa na ranar Litinin ko holewa a ranar Juma’a domin sanya maka karsashin aiki.’’

Nan da nan saƙon ya bazu a shafin na intanet inda mutane sama da dubu 400 suka so shi, sama 7000 kuma suka yi tsokaci.

Mutane da dama sun yaba da tsarin amma kuma wasu sun nuna tababa kan yadda tsarin zai kasance a aikace.

Wani ya rubuta cewa, ‘’wannan tsari ne da zai matsa wa ma’aikaci ya riƙa gama aiki da wuri."

Wani kuma ya rubuta cewa, ‘’tsarin sassauta lokacin aiki’’ka iya tilasta mutum ya riƙa aiki har a ƙarshen mako. Wasu kuma na tambaya ne kan me zai faru idan ya kasance cewa akwai aikin da ba a gama ba kuma ma’aikaci ba zai iya kashe kwamfyutarsa ba.’’

‘’Sai ma’aikaci ya sake kunna kwamfyutar kawai idan ta mutu,’’ in ji Ms Shukla.

Ta ƙara da cewa ba wai tsarin yana nufin cewa lalle sai an bi shi ba ne a’a yana tunatar da abokan aiki ne kawai cewa lokacin tashi daga aiki ya yi, mutum zai iya tafiya gida.

Jami’ar ta ce wasu daga cikin kwastomomi ko masu mu’amulla da su a kamfanin ba su ji daɗin tsarin ba, to amma mu kam mun lamunta da shi, in ji ta.