You are here: HomeAfricaBBC2023 06 26Article 1793030

BBC Hausa of Monday, 26 June 2023

Source: BBC

Kalidou Koulibaly ya koma Al-Hilal ta Saudiyya daga Chelsea

Kalidou Koulibaly Kalidou Koulibaly

Kalidou Koulibaly ya zama ɗan wasa na baya-bayan daga Chelsea da zai koma taka leda a Saudiyya, wannan ya biyo bayan komawar ɗan wasan ƙungiyar Al-Hilal kan kuɗin da ba a bayyana ba.

Ɗan bayan mai shekara 32, ya bi sawun Ruben Neves wajen komawa gasar Saudiyya da wasa, wanda aka saya daga Wolves kan kuɗi fan miliyan 47.

N'Golo Kante da shi ma yake wasa a Chelsea ya amince ya sanya hannu wajen komawa ƙungiyar Al-Ittihad wadda ita ce gwarzuwar gasar Saudiyya, yayin da abokin taka ledarsa Edouard Mendy ke shirin komawa Al-Ahli.

Koulibaly ya koma Chelsea ne daga Napoli a watan Yulin bara kan yarjejeniyar shekara hudu.

Ya koma Stamoford Bridge da taka leda a matsayin wanda ya kware da kwallon turai da kuma ta duniya, bayan taimakawa Napoli da ya yi ta ci Italian Cup a 2020, da kuma ƙasarsa Senegal da ta lashe kofin Nahiyar Afrika a 2022.

Wasa 32 kawai ya buga wa ƙungiyar a duka gasar da ta buga, ya ci kwallo biyu kuma a wasa 23 da ya buga mata a Premier.

"Tun daga wasana na farko zuwa na ƙarshe ina alfahari da sanya bajan ƙungiyar," Koulibaly ya rubuta a Twitter.

"Abin da ya faru a gasar bara ba haka muka so ba, amma ina miƙa godiyata ga magoya baya da kowa a ƙungiyar."

Chelsea ba ta bayyana nawa Al-Hilal ta biya ba kan Koulibaly - amma rahotanni na cewa zai iya kai wa fan miliyan 20.