You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837778

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Juyin mulkin Sojoji ba zai kawo karshen mulkin iyalin Bongo ba in ji wata majiya a fadar shugaban kasa

Hoton tsohon shugaba Ali Bongo Hoton tsohon shugaba Ali Bongo

Juyin mulkin da sojoji suka yi a Gabon abu ne da kai ga zuriar Bongo su ci gaba da mulki wadanda suka shafe shekara 55 suna mulki, kamar yadda wata majiya da ke da kusanci da hambararren shugaban kasa ta shaidawa BBC.

Shi ma”Janarar Brice Oligui Nguema” wani tsantso ne na zuriar Bongo a cewar majiyar wadda ta bukaci a sakaya sunanta saboda dalilan tsaro.

Ta gargadi masu gudanar da shagulgulan juyin mulki da ka da su yi tsammanin samun gagurumin sauyi.

Sojojin kasar sun sha alwashin kawo karshen mulkin Bongo a lokacin da suka kwace mulki.

Sun sanar da juyin mulki ne jim kadan bayan da aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka yi takaddama akai.

A yanzu an yi masa daurin tala-tala a gida.

Sojojin a ranar Asabar sun ce za a sake bude iyakokin kasar bayan an rufe sakamakon juyin mulkin da suka yi a ranar Laraba.

Bayannan majiyarmu sun yi dai- dai da na jagoran ‘yan hammaya Albert Ondo Ossa, wanda ya fadawa kamfanin dilancin labarai na AFP cewa juyin mulki “ juyin juya hali ne na masaurata”, da iyalin Bongo su ka shirya domin ci gaba da rike madafun iko.

Gammayar kungiyoyin da ke goyon bayan Mista Ossa, da ake kira Alternance 2023, wadda ta ce ita ce ta lashe zaben ranar Asabar , ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa kaimi wajan dawo da mulkin farar hula.

" Mun yi farin ciki da aka hambarar da Ali Bongo amma .... muna fatan kasashen duniya za su tashi tsaye don tabbatar da jamhuriya da tsarin dimokuradiyya a Gabon ta hanyar neman sojoji su mika mulki ga farar hula," a cewar Alexandra Pangha, mai magana da yawun Mista Ossa .

Ta kara da cewa shirin rantsar da Janarar Nguema a matsayin shugaban riko a ranar Litinin ba “dai-dai bane”.

Majajlisar Dinkin Dunkya da kasashe makobta da kuma Faransa wadda ta yi Gabon mulki malaka wadda ke da alaka ta kut -da- kut da iyalin Bongo, duk sun yi Alla-wadai da juyin mulkin.

Tarayyar Afrika ta dakatar da Gabon daga cikin kungiyar.

A jawabin da ya yi a wani gidan talibjin da yammacin Juma’a, Janarar Nguema ya ce sojoji za su yi sauri wajan mika mulki ga farar hula amma bai bayana lokacin da za su yi hakan ba.

Ya ce za su kauce wa "kura kuran da aka maimaita a lokacin zabe “ domin mutane da aka saba gani su ci gaba da zama kan karagar mulki.

Sai dai majiyar ta mu ta ce sabon shugaban gwamnatin sojin, wanda shi ne shugaban zaratan sojojin da ke gadin shugaban kasa“ tsantson zuriar Bongo ne“.

Majiyar ta kara da cewa ya na da alaka ta-kut-da -kut da dangin Omar Bongo“, kuma wasu na ganin cewa shi dan uwan Ali Bongo ne.

Omar Bongo ya shafe shekaru 41 yana mulki kafin dansa Ali ya gaje shi bayan rasuwarsa a 2009.

Nasarorin da Ali Bongo ya samu a zabukan da suka biyo baya suna cike da matsaloli sakamakon zargin da 'yan adawa ke yi kan cewa an yi magudi.

Majiyarmu ta bayyana cewa juyin mulkin ya zo da bazata, duk da cewa an rika rade -rade kan janarar Nguema.

“ Abin ya ba mambobinmu mamaki , sai dai a cikin shekaru an rika yada rade- radin cewa da suka yi zargin cewa idan akwai mutun daya tilo da zai iya kawo cikas ga mulkin iyalin Bongo, to wannan mutumin shi ne janarar Nguema.

Ya kasance yana taka "muhimmiyar rawa a iyalin Bongo”.

Ta ce kafin mutuwar Omar Bongo a 2009, Janarar Nnguema ya yi masa alkawarin kula da iyalinsa. Sai dai kuma a lokacin da Ali Bongo ya karbi ragamar mulki, an tura aiki zuwa ofisoshin jakadancin kasar da ke Moroko da Senegal.

" Bayan dawowarsa a 2019,janarar Nguema ya fahimci cewa da’irar mulki ta zarce wadanda suke da kusanci da iyalin , kuma ikon ya fara kubucewa daga hannun iyalin Bongo ,” a cewar majiyarmu.

Wannan ya biyon bayan shanyewar bangaren jiki da Ali Bongo ya yi fama da shi na tsawon wata guda abinda ya janyo kiraye kirayen ya sauka daga mulki.

Juyin mulkin ya sa mutane da dama sun hau kan titunan Libreville babban birnin kasar Gabon domin murna amma majiyarmu ta ce hakan ya faru ne saboda “ sun gaji da iyalin Bongo”

“ Sai dai gaskiyar maganar ita ce juyin mulkin ci gaba ne na tsari daya kawai amma da suna daban”.

Jim kadan bayan sanar da juyin mulkin , an kama mukaraban hambararren shugaban kasar, ciki har dansa Noureddin Bongo Valentin mai shekara 31 da ake zargi da cin amanar kasa da rashawa. Kafar talibijin ta kasar ta nuna hotunansa da wasu makusantan Bongo a gaban akwatunan kudi da ta ce an kwace daga gidajensu. Sai dai ba su ce komai ba kan zargin

Majiyarmu ta ce wannan ba komai bane ila burga ce.

"Ya na son ya ya isar da sako mai karfi ga alummar kasar ta hanyar kama dan shugaban kasa",

" Kowa na murna a yanzu amma kada mu manta cewa shugaban riko ya shafe tsawon shekaru yana cin tuwo tare da Bongo. Ya nada kwarewa sosai kuma ya karfafa fatan mutane , amma ya kamata ‘yan Gabon su kasance a cikin shiri,"in ji majiyarmu.