You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817402

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Juyin mulkin Nijar: 'Abin da ya sa muke maraba da Rasha da kuma korar Faransa'

Hoton alama Hoton alama

A wata alama ta ƙaruwar zaman kiyayya da ƙasashen yamma tun bayan juyin mulki a Nijar, wani ɗan kasuwa ya fito sanye da tufafinsa mai ɗauke da tutar Rasha a cibiyar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum yafi magoya baya.

Tun bayan juyin mulkin, an yi ta samun yaƙin cacar-baka tsakanin sojoji da kuma ƙasashen yamma.

Mista Bazoum babban aboki ne ga ƙasashen yamma, musamman ma wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi, inda ya kuma kulla kyakkyawar dangantaka ta ɓangaren tattalin arziki da ƙasashen.

Akwai sansanin sojin Faransa a Nijar, wadda ta kasance ƙasar da tafi samar da uranium a duniya. Man fetur na da matukar muhimmanci ga makamashin nukiliya, inda rabinsa ke tafiya Turai, musamman ma a ƙasar Faransa.

Tun bayan da Janar Abdourahamane Tchiani ya hamɓarar da shugaban ƙasar ta Nijar a ranar 26 ga watan Yuli, an yi ta yawo da tutocin Rasha a kan tituna.

Dubban mutane ne suka fita zanga-zanga a Yamai, babban birnin ƙasar a ranar Lahadi, inda wasu suka yi ta ɗaga tutocin Rasha har ma da far wa ofishin jakadancin Faransa.

Alamu sun nuna cewa masu ɗaga tutocin Rashan na yaɗuwa a faɗin ƙasar.

Ɗan kasuwar, wanda yake zaune a birnin Zinder, ya buƙaci a sakaya sunansa saboda wasu dalilai inda ya kuma ce a dishe fuskarsa.

"Ni mai goyon bayan Rasha ne sannan bana son Faransa," in ji shi. "Tun ina karami, nake adawa da Faransa.

"Sun ci da guminmu da ɗebe mana arziki kamar uranium da man fetur da zinare. Ƴan Nijar masu karamin karfi ba sa samun cin abinci sau uku a rana saboda Faransa."

Ɗan kasuwar ya ce dubban mutane sun shiga cikin zanga-zangar da aka yi a birnin Zinder ranar Litinin domin goyon baya sojojin da suka hamɓarar da gwamnati.

Ya ce ya tambayi wani tela da ya ɗauki kaya msu alamar tutar Rasha na fari da shuɗi da kuma ja domin ya yi masa ɗinki da shi, inda ya musanta cewa wasu kungiyoyi masu goyon bayan Rasha sun sayi kayan.

Nijar ƙasa ce mai mutane miliyan 24.4, inda mutum biyu cikin biyar ke rayuwa cikin talauci, inda suke kashe kasa da $2.15 a rana.

Shugaba Bazoum ya shiga ofis ne a 2021 bayan samun nasara a zaɓen da ka ayi da kuma miƙa mulki cikin sauki karo na farko a ƙasar tun samun ƴancin kai a 1960.

Sai dai gwamnatinsa ta fuskanci hare-hare na masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da ISIS da kuma al-Qaeda waɗanda ke cin karensu ba bu babbaka a yankin Hamadar Sahara zuwa kudanci.

Bayan matsin lamba na hare-haren masu iƙirarin jihadi, sojoji da ke makwaɓtan Nijar ɗin wato Mali da Burkina Faso, waɗanda su ma Faransa ta yaye, sun hamɓarar da gwamnatocinsu a ƴan shekarun nan, inda suka ce hakan zai taimaka wajen faɗa da mayaƙa.

Kamar Nijar, A baya dukkan ƙasashen na ɗauke da sojojin Faransa waɗanda ke taimaka musu wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi, daga bisani ra'ayin kin jinin Faransa ya karaɗe faɗin yankin, inda dukkan mutane daga ƙasashen uku suka fara zargin Faransa da rashin ƙoƙari wajen dakatar da hare-haren.

Bayan karɓe iko da sojoji suka yi a Mali, nan da nan suka yi maraba da sojojin hayan Rasha na Wagner, inda tun da farko sai da suka tilastawa sojojin Faransa ficewa da kuma buƙatar dubban sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD barin ƙasar.

Duk da cewa an ci gaba da samun hare-haren masu iƙirarin jihadi a Mali, sojojin da ke mulki a Burkina Faso su ma sun koma tare da kulla alaƙa da sojojin Wagner da kuma korar dubban dakarun Faransa.

Gwamnatin Shugaba Bazoum ta sha haramta ra'ayin kin jinin ƙasar Faransa a Nijar.

Kungiyoyin kare hakkin fararen hula da dama sun fara yaɗa zanga-zangar kin jinin Faransa a tsakiyar 2022, lokacin da gwamnatin shugaba Bazoum ta amince da mayar da dakarun Barkhane zuwa Nijar bayan da aka ba su umarnin ficewa daga Mali.

Ja gaba cikinsu shi ne ƙungiyar M62, wadda ƙungiyar masu fafutuka ta haɗaka, na ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin kwadago suka kafa a watan Agustan 2022.

Sun jagoranci kiraye-kirayen adawa da tsadar rayuwa, rashin shugabanci da kuma kasancewar sojojin Faransa.

Hukumomin Nijar sun haramta ko kuma soke zanga-zanga da dama da kungiyar suka shirya yi har ma da ɗaure shugabansu Abdoulaye Seydou na tsawon wata tara a watan Afrilun 2023 saboda "tayar da zaune tsaye".

Sai dai alamu sun nuna cewa M62 ta sake dawowa bayan hamɓarar da Shugaba Bazoum.

A wani abu da ba a saba gani ba, gidan talabijin ɗin ƙasar ya ruwaito cewa kungiyar na shirya mambobinta domin yin gagarumar zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki, da kuma yin Alla-wadai da takunkumi da shugabannin ƙasashen Afrika ta yamma suka kakaba wa ƙasar bayan juyin mulki.

Ba bu dai tabbacin cewa ko kungiyar na alaƙa da sojojin da suka kifar da gwamnati waɗanda aka fi sani da Majalisar Ceton Ƙasar.

Sai dai ita ce ke shirya zanga-zangar da za a yi a ranar Lahadi, tare da haɗin gwiwar wasu ƙananan kungiyoyin fararen hula kamar Kungiyar fafutukar dimokuraɗiyya ta CCLD da kuma Kungiyar Matasan Nijar.

A can Zinder, ɗan kasuwar mai goyon bayan Rasha na da fata mai kyau na cewa Rasha za ta taimakawa ƙasarsa.

"Ina son Rasha ta taimaka mana da tsaro da kuma abinci," in ji shi. "Rasha za ta samar mana da fasaha domin bunƙasa aikin gonar mu."

Sai dai Moutaka, wada ya kasance manomi da ke zaune a Zinder, ya yi watsi da hakan tare da cewa juyin mulkin labari ne mara daɗi ga kowaye..

"Ba na goyon bayan zuwan dakarun Rasha cikin ƙasar nan saboda dukkansu Turawa ne kuma ba bu wanda zai taimake mu," in ji shi. "Ina son ƙasata, ina kuma fatan cewa za mu samu zaman lafiya."