You are here: HomeAfricaBBC2023 06 25Article 1792397

BBC Hausa of Sunday, 25 June 2023

Source: BBC

Juventus na son £52m kan Chiesa, Man Utd na farautar Onano

Federico Chiesa Federico Chiesa

Juventus na bukatar fam miliyan 52 ga duk wanda yake son sayen Federico Chiesa mai shekara 25, yayinda Liverpool ke nuna matsuwarta kan ɗan wasan na Italiya da ke buga gaba, wanda kuma ake ganin Bayern Munich da Paris Saint-Germain na zawarci. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)

Manchester United na farautar mai tsaron raga ɗan kasar Kamaru da Inter Milan Andre Onana, mai shekara 27, yayinda ake ganin ɗan kasar Sifaniyar nan David de Gea, mai shekara 32 na son bankwana da Old Trafford a wannan kakar. (90min)

United na kuma nazari kan mai tsaron raga a Porto da Portugal Diogo Costa, mai shekara 23, da kuma na Brentford David Raya, shi kuma mai shekara 27. (Sky Sports)

Ɗan wasan tsakiya a Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 27 ya kasance wanda Bayern Munich ke hari a yanzu. (Bild - in German)

Tottenham na zawarcin ɗan wasan Juventus da Brazil Gleison Bremer, mai shekara 26. (Telegraph - subscription required)

West Ham na iya sadadu da tayin Arsenal na fam miliyan 100 kan kyeftin dinta Declan Rice, mai shekara 24. (Mail)

Ɗan wasan Sifaniya Cesar Azpilicueta, mai shekara 33 ya amince da yarjejeniyar shekara biyu da Inter Milan bayan watsi da tayin Bayern Munich. (90min)

Borussia Dortmund na iya shiga zawarcin ɗan wasan Chelsea da Ingila Conor Gallagher mai shekara 23, domin maye gurbin Jude Bellingham. (Bild via Caught Offside)

Kocin Fulham Marco Silva, mai shekara 45, ba zai amince da tayi mai gwaɓi da yake samu daga kungiyar Saudiyya ta Al Hilal ba. (Sun)

Crystal Palace na zawarcin ɗan wasan Torino mai shekara 23 Perr Schuurs wanda ke samun tayi daga kungiyoyi irinsu Arsenal, Tottenham, Liverpool da Manchester United. (The Athletic)

Ɗan wasan Palace da Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 30 ya ja hankalin Lazio adaidai lokacin da yarjejeniyarsa ke karewa a wannan watan. (Sky Sports Italia - in Italian)

Arsenal ta cimma yarjejeniyar baka a sayo ɗan wasan tsakiya a Belgium Romeo Lavia, mai shekara 19 daga Southampton. Matashin ɗan wasan kuma ya ja hankalin Chelsea da Liverpool da Manchester United. (Football insider)

Kocin Celtic Brendan Rodgers, na kokarin cimma yarjejeniya da ɗan wasan Australia da Melbourne City, Marco Tilio, 21. (Daily Record)

Fulham na son fam miliyan 35 kan ɗan wasan Amurka Antonee Robinson, mai shekara 25, wanda ke samun tayi daga Newcastle da Marseille. (Evening Standard)

Manchester United na nazarin bai wa ɗan wasan Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 18 riga mai lamba 7, wanda Cristiano Ronaldo ya kasance na karshe da ya yi amfani da ita a kungiyar. (Manchester Evening News)

Kocin Aston Villa Unai Emery na farautar Tyler Adams mai shekara 24 a wannan kaka. (The Athletic)