You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837763

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Juan Mata ya koma Vissel Kobe ta Japan

Tsohon dan kwaƙlon tawagar Sifaniya, Juan Mata Tsohon dan kwaƙlon tawagar Sifaniya, Juan Mata

Tsohon dan kwaƙlon tawagar Sifaniya, Juan Mata ya koma Vissel Kobe ta Japan a matakin mara kungiya.

Mai shekara 35 tsohon dan kwallon Chelsea da Manchester United, kwantiraginsa ya ƙare a Galatasaray ranar 1 ga watan Yuli.

Ya taimaka wa Galatasaray lashe babban kofin tamaula a gasar Turkiya a kakar da ta wuce, amma ba a saka shi a wasa sosai ba.

Mata yana cikin 'yan kwallon tawagar Sifaniya da suka lashe kofin duniya a 2010.

Ya kuma ɗauki Champions League a Chelsea, ƙungiyar da ya koma daga Valencia da lashe Europa League da FA Cup a ƙungiyar Stamford Bridge da kuma Manchester United.