You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829093

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

John Stones zai yi jinyar makonni in ji Guardiola

John Stones John Stones

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya tabbatar da cewa mai tsaron baya, dan John Stones ba zai buga wasa ba har sai an dawo hutun wasannin kasa da kasa.

Stones, mai shekaru 29, ya samu rauni a wasannin share fagen tinkarar kaka bana, kuma bai buga wasanni biyu na farko da City ta yi a gasar Premier ba.

Wato bai yi karawar da City ta doke Burnley da kuma Newcastle United ba a Premier League.

Haka kuma baya cikin 'yan wasan da City ta lashe Uefa Super Cup, bayan da ta doke Sevilla a bugun fenariti da cin 5-4, bayan da suka tashi 1-1.

Za a gudanar da hutun wasannin kasa da kasa ne tsakanin ranar 4 da 12 ga watan Satumba.

Stones ba zai iya buga wasan da Ingila za ta yi da Ukraine a wasan neman shiga gasar cin kofin Turai da Ukraine da wasan sada zumunta a watan gobe.

Kungiyar har ila yau ta rasa babban dan wasanta na tsakiya Kevin de Bruyne, wanda aka yi masa tiyata a kafarsa kuma zai yi jinyar watanni hudu